Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya gana da ’yan uwan wadanda fashewar kayayyakin hada bam ta ritsa da su a Kano kwannan nan.
Buhari ya gana da su ne a Fadar Sarkin Kano yayin da ya ziyarci Kanon domin halartar bikin Sojojin Sama a ranar Litinin.
- Ambaliyar ruwa ta kashe mutum 57 a Bangladesh da Indiya
- Sheikh Ibrahim Khalil ya zama dan takarar Gwamnan Kano a ADC
Shugaban ya kuma yi amfani da damar wajen jajanta wa iyalan marigayan da Sarkin Kano da ma Gwamnatin Jihar Kano.
Sa’ilin da yake jawabi yayin ziyarar, Gwamna Kano ya ce gwamnatin jihar ta ba da diyyar miliyan tara ga ’yan uwan marigayan, sannan miliyan biyu ga mutum 10 da suka ji mummunan rauni, sai kuma miliyan daya ga wadanda rauninsu bai tsananta ba.
Sai kuma cibiyar cinikayya ta African Centre da ta samu milioyan biyu, makarantar da ke kusa da wurin (Winners Academy) wanda lamarin ya rutsa da wasu dalibanta ta samu miliyan N1.
Idan dai ba a manta ba, Aminiya ta ruwaito yadda fashewa mai karfi ta auku a yankin Sabon Gari a Jihar Kano, lamarin da ya yi ajalin mutum tara tare da jikkata wasu da dama.
Daga nan, Buhari ya yi amfani da damar wajen yi wa Najeriya fatan samun nagartattun shugabanni yayin zabe mai zuwa.