✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buhari ya gana da Tinubu da Bisi Akande gabanin taron APC

Buhari ya gana da su don jinjina musu kan irin goyon bayan da suke bai wa gwamnatinsa.

Shugaba Muhammadu Buhari ya karbi bakuncin jiga-jigan jam’iyyar APC a wata liyafa da ya shirya musu a Fadar Shugaban Kasa ranar Alhamis da dare, gabannin babban taron jam’iyyar da za a gudanar ranar Asabar.

Aminiya ta gano Buhari ya shirya liyafar cin abincin ne don nuna godiyarsa ga jiga-jigan jam’iyyar kan irin goyon baya, hadin kai da fahimtar da suka nuna ga gwamnatinsa.

Kazalika, ganawar da Shugaba Buhari ya yi da su na da alaka da kokarin ganin an gudanar da babban taron jam’iyyar na kasa cikin lumana da kuma samun kyakkyawan sakamako.

Liyafar ta samu halartar shugaban riko na farko na APC, Cif Bisi Akande; Uban jam’iyyar, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu; Tsohon shugaban jam’iyyar, Dokta Ogbomnaya Onu; Tsohon Gwamnan Imo, Rochas Okorocha; Tsohon Gwamnan Kano, Sanata Ibrahim Shekarau da kuma tsohon Gwamnan Jihar Sakkwato, Aliyu Magatakarda Wamako.

Sauran sun hadar da Gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, Gwamnan Katsina, Aminu Bello Masari; da Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi.

Shugaban Riko da Tsare-tsaren Babban Taron Jam’iyyar APC, Gwamna Mai Mala Buni na Jihar Yobe da Sakataren Gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha, su ma sun halarci liyafar.

Kafin taron liyafar, Buhari ya gana da gwamnonin APC da ’yan takarar shugabancin jam’iyyar na kasa, da ’yan Majalisar Dattawa, gabanin babban taron da za a yi a ranar Asabar.