Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya gana da sabbin Hafsoshin Tsaron Najeriya.
A ranar Laraba ya yi ganawarsa ta farko da sabbin Manyan Hafsoshin Tsaron, kasa da awa 24 bayan ya nada su.
- An girke sojoji mata 200 a hanyar Abuja-Kaduna
- Kotu ta ba mayu awa 24 su warkar da mara lafiya
- Na yi wa mata 50 fyade da fashi a gidaje 100
“Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya gana da sabbin Manyan Hafsoshin Tsaro a fadar Shugaban Kasa da ke Abuja a yau din nan,” kamar yadda Hadimin Shugaban Kasa kan Shafukan Sa Da Zumunta, Bashir Ahmad ya sanar.
Sai dai kuma babu bayani game da abun da suka tattauna a zaman nasu na farko bayan nadin manyan hafsoshin.
Fadar Shugaban Kasa ta sanar da sauya shugabancin Rundunonin Sojin Najeriya ne a ranar Talata a wata sanarwa da yawancin mutane ga gani a matsayin ba-zata kuma abin da ya dace.
Akasarin ’yan Najeriya sun yi maraba da sallamar tsoffin Manyan Hafsoshin da ake zargi da gazawa wajen magance matsalar tsaron da ta addabi sassan Najeriya.
Akasararin wadanda Aminiya ta zanta da su sun shawarci sabbin jagororin da su sauya salon yaki da ta’addanci da sauran matsalolin tsaro a sassan kasar.
Najeriya na fama da matsalar ta’addancin Boko Haram/ISWAP a yankin Arewa ta Gabas, musamman Jihar Borno, Yobe da Adamawa.
Hare-haren ’yan bindiga masu garkuwa da mutane da satar dabbobi sun addabi yankin Arewa ta Yamma da Arewa ta tsakiya mai fama da rikicin manoma da makiyaya da rikicin kabilanci.
A Kudu Maso Gabas, ’yan taratsin kafa kasar Biafra na IPOB na neman hana zaune tsaye, yayin da masu fasa butun mai da fashi a teku ma ke haifar da damuwa musamman a Kudu maso Kudu da kuma Kudu maso Yamma.