✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Buhari ya gana da mahaifin Sarkin Qatar a Doha

Buhari da ’yan tawagarsa sun gana da mahaifin Sarkin Qatar, Sheikh Hamad Bin Khalifa Al Thani.

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da ’yan tawagarsa sun gana da mahaifin Sarkin Qatar, Sheikh Hamad Bin Khalifa Al Thani, a birnin Doha a ranar Talata.

Cikin wadanda suka rufa wa Shugaba Buhari a lokacin ganawar sun hada da jakadan Najeriya a kasar Qatar Ambasada Yakubu Ahmed.

Shugaba Buhari da tawagarsa na gana wa da mahafin sarkin Qatar a Doha
Shugaba Buhari a lokacin da yake tattauna wa mahaifin sarkin Qatar
Mele Kyari na gaisawa da mahaifin sarkin Qatar
Hadi Sirika na gaisawa da mahaifin sarkin Qatar
Shugaba Buhari yayin isowarsa fadar mahaifin sarkin Qatar
Ambasada Yakubu Ahmed na gaisawa da mahaifin Sarkin Qatar

Sauran sun hada da Shugaban Kamfanin mai na Najeriya NNPC, Mele Kolo Kyari da Ministan Sufurin Jiragen Sama, Hadi Sirika.