Shugaban Kasa Muhammadu, Buhari ya gana da Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele, sa’o’i kadan bayan Kotun Koli ta dage sauraron karar da gwamnatocin jihohin Kaduna, Zamfara da Kogi suka shigar na kalubalantar daina amfani da tsofaffin takardun kudi zuwa ranar 22 ga watan Fabrairu.
Hadimin Shugaban Kasa kan Harkokin Yada Labarai, Garba Shehu, ne ya tabbatar wa gidan talabijin na Channels cewa gwamnan CBN ya gana da shugaban kasa.
- Gwamnatin Kano ta lashe amanta kan hukunta masu kin karbar tsoffin kudi
- Sarki Sanusi II ya ziyarci Kano shekara 3 bayan tube rawaninsa
Kwanaki 11 da suka gabata ne Shugaba Buhari ya roki ’yan Najeriya su ba shi kwanaki bakwai domin ya warware matsalar da canjin kudi ta haifar bayan da kungiyar gwamnonin APC ta bukaci ya duba wahalar da mutane ke sha.
Dangane da rade-radin cewa shugaban kasa na shirin tsawaita wa’adin amfani da tsoffin takardun kudi da wata biyu, Garba Shehu, ya ce ba shi da hurumin tabbatar da wannan labari.
Tun da farko Kotun Kolin ta hana Gwamnatin Tarayya aiwatar da wa’adin ranar 10 ga watan Fabrairu na daina amfani da tsofaffin takardun kudi na N200, N500 da N1,000.
A zamanta na safiyar Laraba, kotun ta sake dage shari’ar zuwa ranar 22 ga watan Fabirairu.
Canjin kudin ya bar baya da kura, inda wasu jihohi musamman a Kudancin Najeriya suka fara zanga-zanga, a wasu jihohin kuwa lamarin ya rikide zuwa tarzoma inda aka kone wasu bankunan kasuwanci.
A Jihar Kano kuwa, bankunan kasuwanci ba su bude ba a ranar Laraba, don gudun hari daga bata-gari.
Tuni dai jami’an tsaro suka fara sintiri musamman a kofar birnin wasu manyan bankuna don shirin ko-ta-kwana.