Tsohon Mataimakin Shugaban Majalisar Wakilan Najeriya, Sanata Usman Bayero Nafada, ya ce Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya gama wa yi wa jam’iyyarsu ta PDP kamfe a zaben da ke tafe.
Sanata Bayero Nafada wanda shi ne Babban Daraktan yakin neman zaben Gwamnan Jihar Gombe na PDP, Muhammad Jibrin Barde, ya ce a kwanakin da suka rage a gudanar da zabe Shugaban Kasa, Buhari ya gama wa PDP kamfe saboda irin halin da ya jefa Najeriya a ciki.
- Girgizar kasar Turkiyya: An ceto mutum 3 da rai bayan shafe kwana 13 ba ci ba, ba sha
- 2023: Na fasa takarar Gwamnan Kano a LP, na koma wajen Tinubu – Bashir
Ya bayyana hakan ne a yayin wani taron manema labarai a gidansa da ke Gombe, ranar Asabar, inda ya cewa dan takararsu na Shugaban Kasa, Alhaji Atiku Abubakar, ya fi Bola Tinubu na jam’iyyar APC cancantar Shugabancin Najeriya saboda ya fi shi sanin ciki da wajen kasar.
A cewars,a jam’iyyar APC ta jefa Najeriya da mutanen cikinta a mawuyacin halin rashin iya mulki ga kuma canja kudi da suka suka kara tagayyara al’umma.
Ya ce yanzu mutane da kudinsu sun zama abin tausayi.
Har ila yau Bayero Nafada, ya kara jan hankalin ’yan Najeriya da cewa su kula da kalaman Tinubu da yake cewa idan aka zabe shi zai dora ne daga inda Buhari ya tsaya.
Tsohon dan majalisar ya kuma ce zaben PDP a dukkan matakai ne kawai zai tabbatar da yaki da yunwa da talaucin da ya ce ’yan Najeriya na kuka da su a yanzu.
A kan batun da wasu ke yi cewa ba a kayar da gwamnati mai mulki kuwa, Bayero ya ce ba gaskiya ba ne, saboda ko a Jihar da makwabciyarta ta Bauchi da kuma Zamfara an taba kayar da Gwamnoni masu ci.