✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buhari ya fusata da Babban Banki kan karya darajar Naira

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya fusata da Babban Bankin Najeriya kan bullo da sabon salo na canjin kudi wanda a karshe ya jawo karya darajar…

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya fusata da Babban Bankin Najeriya kan bullo da sabon salo na canjin kudi wanda a karshe ya jawo karya darajar Naira, inda Shugaba Buhari ya nace kan matsayinsa na cewa tsarin ba zai amfani tattalin arzikin Najeriya ba.
A makonnin nan ne Babban Bankin Najeriya (CBN) ya bullo da kasuwar baidaya ta musayar kudi da sunan barin Naira ta kwaci kanta lamarin da ya jawo darajar Naira ta yi muguwar faduwa, inda ya ce har yanzu bai gamsu da alfanun karya darajar Nairar ba.
Bayan wata 16 da Babban Bankin ya amince da canja Dala daya a kan Naira 197 ne bankin ya yi watsi da wannan tsari a ranar 20 ga Yunin bana, domin barin Naira ta gwara kanta da kudin kasashen waje. An rika kukan salon yanke farashi kan kudin musayar a baya ya jawo karancin kudaden musayar inda aka rika sayar da Dalar Amurka kan Naira 300 a kasuwar bayan fage.
Bayan cire wannan shigen an rika sayar da Dala daya kan Naira 282 zuwa Litinin da ta gabata, alhali a wata wasikar sirri da Gwamnan Babban Bankin, Godwin Emefiele ya aike wa Shugaba Buhari ya bayyana cewa “bisa cikakken yakini” Dala za ta daidaita a tsakanin Naira 250 bayan an dan fuskanci zangon rashin karfinta.
Kafin fara aiwtar da wannan tsari na baya, Shugaba Buhari ya sha yin watsi da matsin lambar wasu hukumomi kan ya karya darajar Nairar ciki Hukumar Lamuni ta Duniya (IMF). A lokacin da yake magana a wajen buda-bakin da ya shirya wa manya da shugabannin ’yan kasuwa a ranar Litinin da ta gabata a Abuja, Shugaba Buhari ya ce sam ba ya ji dadin bayanan da yake samu daga Babban Bankin. “A Agusta 1985, ana sayar da Dala daya kan Naira daya da sule uku, amma yanzu sa ka saye ta a kan Naira 300 ko 350. Me muka samu daga haka? Nawa za mu samu daga wannan tabargaza ta karya darajar Naira? Ni ba masanin tattalin arziki ba ne kuma ba dan kasuwa ba, – amma na kasa gamsuwa da bayanan masana tattalin arziki kan haka,” inji Buhari.
A lokuta da dama a kasashen waje kamar Masar da Kenya, Buhari ya ce kara karya darajar Naira yana nufin “Kashe ta ne” kuma ya kalubalanci masana tattalin arziki na Najeriya da masu fashin baki kan kudi su gamsar da shi kan alfanun haka.
Shugaba Buhari ya ce tsarin na Babban Bankin har yanzu bai amfani kasar nan ba, sai ya ce abin da yake faruwa a yanzu ya faru ne sakamakon yadda muka jefa tattalin arzikinmu a ciki. Ya bukaci ’yan kasuwa su samar da aikin yi ta yadda za a fitar da Najeriya daga matsalar rashin aikin yi.