Shugaban Majalisar Dattijai, Sanata Ahmed Lawan ya bigi kirjin cewa tun da Najeriya ta dawo mulkin Dimokuradiyya babu Shugaban Kasar da ya fi Muhammadu Buhari rattaba hannu a kan sabbin kudurorin doka.
Ya bayyana hakan ne yayin da yake karbar kyautar Gwarzon Dan Siyasar 2021 da kamfanin jaridar The Sun ya ba shi a Legas ranar Asabar.
Lawan, a cewar wata sanarwa ta bakin kakakinsa, Ola Awoniyi, a ranar Lahadi ya jinjina wa Shugaban kan yadda ya ce yana da kyakkyawar dangantaka da ’yan majalisa.
Sanata Ahmed Lawan ya ce, “Mu a matsayinmu na majalisa ta tara, ban da muna samun hadin kan Shugaban Kasa wajen tabbatar da bangaren zartarwa da na majalisa sun yi aiki yadda ya kamata, da ba a samu rattaba hannu a kan dukkan wadannan dokokin ba.
“Saboda haka, mun yi amannar cewa dole bangarorin biyu su yi aiki kafada da kafada. Babu laifi a samu sabanin ra’ayi wani lokacin, amma ba ta hanyar da hakan zai kawo koma-baya ga kasa ba,” inji Shugaban Majalisar.
Ya ce Majalisar mai ci ta yi zarra matuka idan aka kwatanta ta da takwarorinta na baya saboda nasarorin kammala kudurorin da suka shafe shekaru ba a iya amincewa da su ba a zaurenta.