Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya sanar da ware Naira biliyan 470 domin samar da kayan aiki da karatu a jami’o’i a kasafin shekarar 2023.
Da ake gabatar da kasafin a zauren Majalisar Dokoki ta Kasa, Buhari ya bayyana cewa kasafin 2023 na Naira tirilian 19.76ya yi kyakkyawan tanadi domin saukaka wa ’yan Najeriya halin tsadar rayuka.
- Bankin CBN ya bai wa masu kananan sana’o’i tallafin tiriliyan N2.1
- Yadda Tukur Mamu ya hana ceto fasinjojin jirgin kasa —Atta
- NAJERIYA A YAU: Yadda Abinci Ke Kashe ’Yan Najeriya
Buhari ya bayyana cewa kasafin wanda shi ne mafi girma a tarihin Najeirya, “Shi ne na karshe da da zan gabatar wa Majalisar Dokoki ta Tarayya kafin karewar wa’adin mulkina na karshe a ranar 29 ga watan Mayu 2023.”
Ya kuma bayyaan cewa bangaren tsaro da noma da ilimi na daga cikin wadanda aka bai wa fifiko a kasafin nasa.
Buhari ya bayyana wa zaman hadin gwiwar Majalisar Dattawa da Majalisar Wakilai cewa an yi kasafin ne bisa hasashen farashin gangar danyen mai a kan Dala 70 da hasashen samar da ganga miliyan 1.69 a kullum.
Ya bayyana cewa za a samu gibin Naira tiriliyan 8.8 wanda ake sa ran cikewa daga kudaden da za a samu daga banagaren daga rancen kasashen ketare da kuma cefanar da kamfanonin gwamnati.
Kasafin ya yi hasashen hauhawar farashin kaya a kan kashi 6.31 cikin 100 da kuma karuwar tattalin arziki na cikin gida da kashi 3.75 cikin 100.
Ya yaba wa Majalisa bisa hadin kai da bangaren zartarwa ya samu daga gare ta, wajen aikin kasafin kudi da kuma nasarorin da aka samu.
Tun a shekarar 2022 Najeriya aka rika kammala aiki da amincewa da kasafin kudi kafin karshen shekara.
A jawabinsa kafin bayar da alkalumun kadaden da aka ware a kasafin na 2023, Buhari ya yi waiwaye kan bangarorin da yace gwamnatinsa ta yi nasara wajen aiwatar da kasafin kudi musamman a shekaru uku da suka gabata.
Bangarorin a cewarsa sun hada da na wutar lantarki, man fetur da iskar gasa, tallafin kyautata rayusa da samar da ayyukan yi, bangaren noma da kuma kara kudaden shigar gwamnati.
Haka kuma ya sanya hannu kan umarnin shugaban kasa, ciki har da wadanda suka karfafi hukumomin yaki da rashawa da kuma tabbatar da yin komai a fili wajen gudanar da gwamnati da sauransu.