Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya dage ziyarar ta’aziyya da yake hanyarsa ta kaiwa Jihar Zamfara saboda rashin kyan yanayi.
Buhari ya dage ziyarar ce bayan saukarsa a makwabciyar Jihar Zamfara, wato Jihar Sakkwato, inda ya kaddamar da aikin gina masana’antar siminti ta kamfanin BUA.
- Jirgin ’yan sanda ya yi hatsari a Bauchi
- A shekara 7 Gwamnatin APC ta yi ayyukan da Amurka ta kasa
- Buhari ya aza harsashin ginin masana’antar simintin BUA a Sakkwato
A yayin da ake jiran Buhari ya karasa zuwa Jihar Zamfara, gwamnan jihar, Bello Matawalle, ya sanar cewa rashin kyan yanayin sararin samaniya ya hana jirgin shugaban kasar tashi daga Sakkwato, wanda ya tilasta dage ziyarar tasa zuwa Zamfara.
“Shugaban Kasa ya yi magana da ni inda ya bukaci in isar da sakon ban hakurinsa ga al’ummar Jihar Zamfara. Amma ya ce zai sake sa ranar zuwa jihar a makonni masu zuwa, wanda za a sanar a nan gaba,” inji Gwamna Matawalle.
Wakilinmu ya ce sanarwar ta fito ne a yayin da mutanen Jihar Zamfara sun yi dafifin jiran isowar Buhari wanda ke hanyarsa ta kawo musu ziyarar ta’aziyya.
Buhari ya shirya kai ziyarar ce domin jajanta wa al’ummar jihar game da asarar rayukan da aka yi a sakamakon hare-haren ’yan bindiga.