Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya sanya hannu kan yarjejeniya da kasar Siwizaland da kungiyoyin da ke rajin bunkasar kasashe kan dawowa da sanya ido da kuma gudanar da kadarorin sata da ’yan kasar suka mallaka ba bisa ka’ida ba.
Mai baiwa shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin yada labarai da wayar da kan jama’a, Mista Femi Adesina shi ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya sanyawa hannu a ranar Litinin.
Mai magana da yawun shugaban kasar ya ce hakan ya biyo bayan amincewar da majalisar ministocin kasar ta yi da batun.
Ya bayyana cewa dawowa da kadarorin zai karfafa yaki da cin hancin da gwamnatin Buhari take yi tare da samar da kudi ga bangaren kayan more rayuwar kasar.
Ya kara da cewa shugaban ksar ya sanya hannu a wata yarjejeniya da kasar ta yi tsakaninta da kasar Sinagpore don kaucewa maimaita karbar haraji kan kudin shiga .