Shugaba Muhammadu Buhari ya umarci Karamin Ministan Kwadago Festus Keyamo ya ci gaba da shirin daukar ma’aikata 774,000 a fadin Najeriya.
Festus Keyamo ya tabbatar wa wakilinmu a zantawar da suka yi ta waya a cewa Buhari ya ba da umarnin ne a ranar Talata 14 ga watan Yuli.
“Na samu sabon umarni ci gaba da shirin bisa umarninsa, in kuma ci gaba da lura da shirin kamar yadda doka ta tanadar”, a cewarsa.
A baya ministan ya yi cacar bai da ‘yan Majalisar Dattawa a kan aiwatar da shirin wanda majalsiar ta soke bisa zarginsa da yin gaban kansa wajen zabar ‘yan kwamitin mutum 20-20 na daukar aikin da aka kaddamar a ranar 20 ga watan Yuni.
Bayan umarnin Shugaban Majalisar Dattawa Sanata Ahmed Lawan ne Keyamo ya shaida wa wakilinmu cewa shirin zai ci gaba da daukar ma’aikatan a jihohi, kamar yadda aka tsara da farko bayan umarnin na Shugaba Buhari.
“An riga an gama da zaben ‘yan kwamitocin jihohi. Da ma babu abun da ya tsayar da shi”, inji shi.
Shirin daukar ma’aikatan 774,000
Gwamnatin Tarayya ta fitar da shirin ne domin daukar kananan ma’aikatan wucin guda 1,000 a kowacce daga kanan hukumomin Najeriya guda 774.
Ma’aikatan za su yi kanan ayyuka ne na tsawon wata uku a kan albashin N20,000 a duk wata, a shirin da aka ware wa Naira biliyan 52.
Kwamitin mutum 20-20 na masu daukar aikin a kowace jiha na karkashin jagorancin Darekta Janar na Hukmar Samar da Ayyuka (NDE), Nasir Ladan Argungu, karkashin kulawar Karamin Ministan.
Ba ni da masaniya, inji shugaban NDE
Sai dai da wakilinmu ya tuntube shi game da sabon umarnin shugaban kasar na ci ga da daukar ma’aikatan, Nasir Ladan ya ce ba shi da masaniya a kai.
“Ba ni da hurumin cewa komai a kai. Ba ni da labarain umarnin na Shugaban Kasa”, kamar yadda ya shaida wa wakilin namu ta waya a ranar Talata.