✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buhari ya ce a ba wa manoma taraktocin da NASENI ta gyara

Ya ce samun kayan aiki na zamani zai bunkasa amfanin da za a girba

Shugaba Buhari ya ba da umarnin ba wa manoma taraktocin da hukumar NASENI mai kula da kayan kimiya da fasaha, ta gyara domin bunkasa harkar noma a Najeriya.

Mataimakin Shugaban NASENI, Farfesa Muhammad Sani Haruna ya ce umarnin da Buhari ya bayar lokacin ganawarsu kan ayyukan hukumar, ranar Laraba, ya yi daidai da manufar Shugaban Kasar na bunkasa harkar noma.

Ya ce NASENI ta gyara taraktoci masu yawa a cibiyarta da ke Minna, Jihar Neja da hadin gwiwa da kamfanin MECA, Hukumar rage asarar noma ta NIRSAL.

A cewarsa, Buhari ya yaba da kokarin NASENI wurin gyara da kuma kirkiyar na’urori da injinan aikin gona na zamani domin bunkasa harkar noma a Najeriya.

Farfesa Muhammad Haruna ya ambato Buhari na cewa samun takarkoci su ne muhimman kayan noma da za su taimaka wa manoma sarrafa kasa domin samun amfani mai yawa.

Ya ce  Buhari ya kosa manoma su fara amfani da taraktocin kafin damina mai zuwa saboda irin wahalar da manoma marasa kaya aikin zamani ke sha.

A ranar Talata, Buhari ya ba da tabbaci cewa gwamantinsa za ta yi dukkan mai yiwuwa wurin yakar hauhawar farashin kayan abinci  a kasar a shekarar 2021.

“Shugaban Kasa ne Shugaban Kwamitin Daraktocin NASENI; mun zo ne mu yi masa bayanin ayyukan hukumar – nasarorin da muka samu da kuma wuraren da muke bukatar taimakonsa,’’ inji shi.

Ya jaddada aniyar hukumarsa ta samar da ingantattun yaka da injina domin bunkasa tattalin arziki da bangaren masana’antu a Najeriya.

“Bukatarmu kawai shi ne goyon bayan ’yan Najeriya da gwamnatoci comin mu ci gaba da sauke wannan nauyin,’’ a cewarsa.

Ya ce NASENI ta kera babur, babur mai kafa biyu, na’urar zabe mai amfani da hasken rana da kuma jirgi mara matuki da ke amfani da hasken rana domin yin feshi a gonaki, ko aikin sintiri da sauransu.

Tana kuma kera injin rarraba wutar lantarki da kuma na’urar tara karfin hasken lantarki da sauran kaya masu amfani da hasken rana da ake amfani da su a fadin Yammacin Afirka.