Kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa Iqamatis Sunnah JIBWIS, ta yaba wa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a bisa raba wa talakawa hatsi da ya yi albarkacin watan Azumi na Ramadana.
Shugaban JIBWIS na kasa Sheikh Abdullahi Bala Lau ne ya jinjina wa shugaban kasar bisa wannan mataki da ya dauka, wanda a cewar sa zai kawo sauki matuka ga al’umma.
Sheikh Bala Lau ya ce, “AlhamdulilLah, muna jinjina ga shugaban kasa, wannan ba karamin taimaka wa talakawa zai yi ba.
“Kuma muna kira ga hukumomin da alhakin raba wannan kaya ya shafa su hada kai da shugabannin al’umma da suka fi kusa da su kamar malamai da sarakuna wajen raba wannan tagomashi don ganin cewa wannan tallafi ya isa zuwa ga talakawa,” in ji Sheikh Bala Lau.
A makon nan ne dai Gwamnatin Tarayya ta bayar da umarnin a fito da hatsi da yawansa ya kai tan dubu arba’in daga rumbunanta a raba wa ’yan Najeriya domin kawo saukin tsadar kayan abincin da ya addabi kasar.
Shugaba Muhammadu Buhari ne ya ba da umarnin da nufin rage radadin tsadar kayan abinci musamman a watan Ramadan da ake ciki da kuma lokacin bukukuwan Sallah da na Ista suke kara matsowa.
Da yake bayani a Fadar Shugaban Kasa a ranar Talata, Ministan Noma da Raya Karkara, Mohammed Abubakar, ya ce tuni aka kammala aikin fara rabon hatsin ga ’yan Najeriya bisa tsarin da aka yi rabon tan 70,000 na hatsin da gwamnatin ta fitar a lokacin kullen COVID-19 a fadin kasar.
Idan ba a manta ba dai, a watan da ta gabata, Sheikh Bala Lau ya yi kira na musamman ga shugaban kasa da ya bude rumbunan abinci da asusun gwamnati saboda tallafawa al’umma a cikin watan Ramadaan.
Sheikh Lau ya yi wannan kira ne a lokacin da shugaban kasan ya halarci bude babban masallacin da kungiyar JIBWIS ta gina a Abuja.