✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buhari ya bukaci ’yan takara su amince da sakamakon zabe

Buhari ya bukaci INEC da jami'an tsaro da su tabbatar an gudanar da zabe cikin lafiya.

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bukaci ’yan takarar da za su fafata a dukkan matakai da su aminta da sakamakon zaben da Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) za ta sanar.

Shugaba Buhari ya yi wannan kiran ne a taron sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya na ’yan takarar zaben shugaban kasa na 2023 a Cibiyar taro na kasa da kasa da ke Abuja a ranar Laraba.

Buhari ya ja hankalin ’yan siyasa da magoya bayansu, cewa INEC ita ce hukumar da doka ta ba ta ikon bayyana sakamakon zabe.

“Duk dan takarar da sakamakon bai kwanta masa a rai ba, kamata ya yi bi tsarin shari’a, kuma dole ne mu bai tsarin shari’armu kwarin gwiwa.

“Ina sake rokon ’yan takara da su yi biyayya ga yarjejeniyar da suka sanya hannu a yau.

“Ina sake tunatar da daukacin ‘yan Najeriya cewa wannan ita ce kasa daya tilo da muke da ita, kuma dole ne mu yi duk abin da ya dace don kare ta, hadin kai da zaman lafiya.

“Bai kamata a tada tarzoma ba bayan sanar da sakamakon zabe. Duk korafe-korafe, na sirri ko na sarari, a kai su ga kotun da abin ya shafa,” inji shi.

Buhari ya tabbatar wa ’yan Najeriya cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da yin iya kokarinta wajen ganin an gudanar da zabe mai inganci.

“Tun lokacin da na hau mulki, mun yi aiki tukuru don ganin mun gudanar da sahihin zabe cikin lafiya da kwanciyar hankali.

“Za mu ci gaba da yin aiki ba tare da tsangwama ba, tare da ba da damar bin doka da oda a kan abin da ya shafi siyasa.

“Za mu iya buga misali da zaben da aka gudanar a jihohin Edo, Ondo, Anambra, Ekiti da Osun.

“Mun bai wa ’yan Najeriya damar zabar wanda suke so ya mulke su. Mun himmatu ga wannan a cikin wannan gwamnati,” in ji shi.

Don haka shugaban ya tabbatar wa INEC da hukumomin tsaro da duk hukumomin da abin ya shafa alhakin gudanar da zaben da zai kafa tarihi.