✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buhari ya bukaci musulmi su yi amfani da koyarwar Ramadan 

Shugaba Muhammadu Buhari, ya bukaci musulmin Najeriya da su yi amfani da darussan da watan Ramadan ya koyar. Shugaban ya kuma bayyana gamsuwarsa game da…

Shugaba Muhammadu Buhari, ya bukaci musulmin Najeriya da su yi amfani da darussan da watan Ramadan ya koyar.

Shugaban ya kuma bayyana gamsuwarsa game da zaben 2019  da aka yi a Najeriya cikin zaman lafiya.

A sakon barka da Sallah da shugaba Buhari ya yi wa ‘yan Najeriya ya jinjinawa hukumar zabe mai zaman kanta ta Najeriya INEC game da kyakkyawan aikin da suka yi duk da yake akwai wasu kalubalen demokuradiyya.