✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buhari ya bude kamfanin kyankyasar kaji a Kaduna

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari  ya bude katafaren kamfanin kyankyasar kaji wanda ake kira da turanci “Olam Integrated Poultry Farm and Feeds Mill” a jihar Kaduna. Da…

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari  ya bude katafaren kamfanin kyankyasar kaji wanda ake kira da turanci “Olam Integrated Poultry Farm and Feeds Mill” a jihar Kaduna.
Da yake bude kamfanin jiya, Buhari ya bayyana cewa kasar na fita da masassarar tattalin arzikin da ta shiga.
Kamfanin wanda aka kashe biliyoyin Naira wajen gina shi yana tsakanin kyauyukan Chikpiri- Gabas da Gwagwada da ke jihar Kaduna, shi ne kamfani kyankyasar kaji da abincin kaji mafi girma a Afirka.
Shugaban ya ce gwamnati ba za ta yi kasa a gwiba har sai kowane ’yan Najeriya ya sami wadataccen abinci
Ya kara da cewa kamfani kamar Olam zai bunkasa tattalin arzikin Najeriya tare da samar da ayyukan yi.