✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buhari Ya Bude Gadar Neja Ta Biyu

Buhari ya ce an yi amfani da kudaden da aka kwato a Amurka ne wajen sake gina gadar.

A ranar Laraba Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, ya sake bude Gadar Neja ta Biyu na wucin gadi domin saukake zirga-zirga zuwa yankin Kudu maso Gabas a lokacin bukuwan Kirsimeti.

Tuni dai matafiya da masu abubuwan hawa suka yaba da bude gadar, musamman a wannan lokaci da ake samun yawan tafiye-tafiye.

Da yake jawabi a bisa wakilicin Ministan Ayyuka, Babatunde Fashola (SAN), Shugaba Buhari ya nusar da masu abubuwan hawa da a yi tuki tare da lura.

Buhari ya ce, galibin kudin da aka yi amfani da shi wajen sake gina gadar, kudin kasa ne da gwamnati ta kwato bayan wasu sun sace sun kai Amurka sun boye.

Ya kara da cewa, an bai wa gadar muhimmanci ne domin ci gaba da kare rayuka da dokiyoyin al’umma.

Don haka ya ce, da wuya a cimma manufar gina gadar muddin jama’a ba za su kula da yadda za su yi amfani da ita ba.