✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buhari ya bai wa Tinubu lambar GCFR

Buhari zai mika wa Tinubu mulki a ranar 29 ga watan Mayu.

Shugaban Najeriya mai barin-gado Muhammmadu Buhari ya bai wa wanda zai gaje shi, Bola Ahmed Tinubu, lambar girma mafi daraja ta kasar wato GCFR a takaice (Grand Commander of the Order of the Federal Republic).

Haka kuma,Buharin ya bai wa mataimakin shugaban kasar mai jiran-gado, Kashim Shettima lambar girmamar ta biyu a daraja wato GCON a takaice (Grand Commander of the Order of Niger).

Shugaban ya ba su lambobin da kuma takardun mulki ne a Abuja, a shirye-shiryen da ake yi na rantsar da sabuwar gwamnati, ranar Litinin 29 ga watan nan na Mayu, bayan kammala wa’adinsa na biyu na shekara hudu-hudu.

Za a rantsar da sabuwar gwamnatin ne bayan zaben 2023, wanda dan takarar jam’iyyar APC mai mulki Bola Tinubu ya yi nasara.

Sai dai kuma Atiku Abubakar na PDP wanda ya zo na biyu da Peter Obi na jam’iyyar Labour wanda ya zo na uku tare da jam’iyyunsu suna kalubalantar nasarar a kotu.