A yayin zaman Majalisar Zartarwa da Shugaban Buhari ya jagoranta a ranar Laraba, ya ba da umarnin fara aikin titin Dawakin Tofa zuwa Gwarzo a Kano a kan Biliyan N62.7.
Ministan Ayyuka da Gidaje, Babatunde Fashola ya bayyanawa manema labarai cewa aikin zai dauki tsawon wata 24 kafin a kammala shi.
- Ganduje zai gina rukunin gidaje a masarautun Kano
- Za a kwace aikin titin Kano-Abuja daga Julius Berger
- Buhari ya bukaci a kawo rahoton hatsarin jirgi a Legas
- An bude jigilar jiragen sama zuwa kasashen waje
Ministan Labarai da Raya Al’adu, Lai Mohammed ya ce za a kashe kimamin N470,263,037 domin gyara da sanya sabbin na’urori a filin tashi da saukar jirage na Legas.
Lai Mohammed wanda ya wakilci Ministan Sufurin Jiragen Sama, Hadi Sirika, ya ce an ba wa kamfanin Intelligent Transportation System Limited kwangilar aikin, wanda ake sa ran kammala shi cikin wata shida.
Ya kara da cewa fadada aikin na da matukar muhimmanci saboda dibar sabbin ma’aikata da aka yi a filin tashin jiragen.