Shugaba Muhammadu Buhari, ya yi son barka tare da bayyana farin cikinsa dangane da sasanta rikicin cikin gida da ya kunno kai a masarautar Sarki Abdallah II Bin Al-Hussein na Jordan.
Shugaban kasar ya bayyana hakan ne cikin wata wasika da ya aike wa masarautar kamar yadda mai magana da yawunsa, Mallam Garba Shehu ya zayyana wa manema labarai cikin birnin Abuja a ranar Alhamis.
- Shugabannin ‘yan bindiga 4 sun mika wuya a Katsina
- Shin DSS ce ta azabtar da direban Buhari har ya mutu?
Cikin wasikar mai dauke da sa hannunsa, Buhari ya ce ya kadu yayin da samu labarin rikicin ’yan uwan juna da kunno kai a masarautar, amma a yanzu yana farin cikin dangane da dinke baraka a masarautar.
Wasikar ta ce, “A yayin da nake nan a Landan inda nake gajeren hutu, na damu matuka bayan rahoton da kafofin watsa labarai suka yada na cewa ana kokarin hargitsa masarautar Hashemite.”
“Jagorancinka tun bayan hawanka karagar mulki, ya zamo abun alfahari ga sauran kasashen duniya, kuma dangartakar da ke tsakanin Najeriya da Jordan a kullum kara kyau take yi kuma muna godiya da irin rawar da kake takawa wajen inganta alakarmu.”
A karshe, Shugaba Buhari ya sake jaddada girmamawa da kuma mutuntawar da yake yi wa masarautar Jordan.
A makon da muke ciki ne Sarki Abdallah ya amince a sulhunta sabanin cikin gida tsakaninsa da dan uwansa, Yarima Hamzah, wanda aka zarga da yunkurin kifar da gwamnatinsa aka kuma yi masa daurin talala.
A baya dai Gwamnatin Jordan tana zargin Yarima Hamza, wanda tsohon mai jiran gadon sarautar kasar ne, da hadin bakin da ya haifar matsalar tsaro a kasar, lamarin da ya janyo aka tsare shi tare da wasu mutane 16.
Gidan Rediyon Faransa ya ruwaito cewa, kawun Sarki Abdallah, Yarima Hassan ne ya ja ragamar sasanta rikicin gidan a masarautar ta Hashemite.
Kafin sasancin da aka yi, Yarima Hamzah ya ce ba zai yi biyayya ga wani umarnin daga fadar ba.