Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya aike da karin kasafin kudi na Naira biliyan 819.5 ga Majalisar Dokoki ta Kasa domin amincewa.
Ana sa ran za a bai wa kasafin lamuni ta hanyar samun kudaden cikin gida.
- Kakakin Majalisar dokokin Taraba ya ajiye mukaminsa
- Cin mutunci kawai abokan hamayya ta suka iya — Tinubu
Hakan zai kara gibin kasafin kudin zuwa Naira tiriliyan 8.17.
A cewar wata wasika da Kakakin Majalisar Wakilai, Femi Gbajabiamila ya karanta a zauren majalisar ranar Laraba, karin kasafin kudin zai magance matsalar abinci, biyo bayan mummunar ambaliyar ruwa da aka samu a fadin kasar nan da kuma tabarbarewar tattalin arziki.
Shugaban ya ce an tsara karin kasafin ne kan bukatar kammala muhimman ayyukan Gwamnatin Tarayya da take yi, kamar ayyukan madatsun ruwa da manyan hanyoyi.
A ranar 31 ga watan Disamba, 2021 Buhari, ya rattaba hannu kan kudirin kasafin kudin 2022 na Naira tiriliyan 17.126 bayan da babban mai taimaka masa na musamman kan Majalisar Dattawa, Sanata Babajide Omoworare, ya gabatar a zauren majalisar.
Shugaban ya ce zai waiwayi Majalisar Dokoki kan bukatar yi mata gyara domin ganin cewa muhimman ayyuka da gwamnatinsa ta sa gaba ba su samu koma-baya ba sakamakon rage kudaden da ake kashewa.
Ya kara da cewa, a yayin gabatar da kudurin kasafin kudin na 2022, ya bayyana cewa kasafin zai kasance mai matukar muhimmanci a kokarin gwamnatinsa na kammala muhimman ayyuka da kuma inganta rayuwar ‘yan Najeriya baki daya.