✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Buhari na neman majalisa ta amince da kara shekarun ritayar malamai zuwa 65

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, a ranar Laraba ya aike da kudurin da ke neman Majalisar Dokoki ta Tarayya ta kara shekarun ritayar malaman makaranta daga…

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, a ranar Laraba ya aike da kudurin da ke neman Majalisar Dokoki ta Tarayya ta kara shekarun ritayar malaman makaranta daga 60 zuwa 65.

Kudurin mai taken “Hadakar shekarun ritayar malamai a Najeriya na 2021” ya kuma nemi a kara shekarun aikin malaman daga 35 zuwa 40.

Bukatar hakan dai na kunshe ne a cikin wata wasika da Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Ahmed Lawan ya karanta a zauren majalisar ranar Laraba.

Shugaba Buhari ya ce sabuwar dokar za ta inganta tsarin aikin malaman ta hanyar kara shekarun ritayar tasu. 

A cewarsa, yunkurin karin ya yi daidai da tanadin Kundin Tsarin Mulkin Najeriya na shekarar 1999 Sashe na 58 (2).