Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, a ranar Laraba ya aike da kudurin da ke neman Majalisar Dokoki ta Tarayya ta kara shekarun ritayar malaman makaranta daga 60 zuwa 65.
Kudurin mai taken “Hadakar shekarun ritayar malamai a Najeriya na 2021” ya kuma nemi a kara shekarun aikin malaman daga 35 zuwa 40.
- Najeriya na zargin Twitter da hannu a fafutikar kafa kasar Biyafara
- Zan ba wa masu tada tarzoma a Najeriya mamaki — Buhari
Bukatar hakan dai na kunshe ne a cikin wata wasika da Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Ahmed Lawan ya karanta a zauren majalisar ranar Laraba.
Shugaba Buhari ya ce sabuwar dokar za ta inganta tsarin aikin malaman ta hanyar kara shekarun ritayar tasu.
A cewarsa, yunkurin karin ya yi daidai da tanadin Kundin Tsarin Mulkin Najeriya na shekarar 1999 Sashe na 58 (2).