✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buhari tsohuwar zuma ne – Fadar Shugaban kasa

Fadar Shugaban kasa ta bayyana cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari tsohuwar zuma ne da zai yi amfani da yawan shekarunsa wajen magance matsalolin kasar nan.…

Fadar Shugaban kasa ta bayyana cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari tsohuwar zuma ne da zai yi amfani da yawan shekarunsa wajen magance matsalolin kasar nan.

Mai ba Shugaban kasa Shawara ta Musamman kan Harkokin Watsa Labarai, Mista Femi Adesina ne ya bayyana haka a wani martani da ya fitar a shekaranjiya Laraba, game da kiran da wata kungiyar PDP ta yi na Shugaban ya sauka saboda yawan shekaru.
kungiyar dai ta yi wannan kira ne bayan da aka ruwaito shi yana shaida wa ’yan Najeriya mazauna Afirka ta Kudu cewa yawan shekarun zai takaita kazar-kazar dinsa.
Sai dai Shugaba Buhari ya ce yawan shekaru ba zai shafi aikinsa na shugabancin Najeriya ba, inda ya ce, a matsayinsa na mai shekara 72, yana da gogewa da hikima da hakuri da danne zuciya da yawan shekaru ke samarwa, kuma zai yi amfani da wadannan halaye wajen gudanr da shugabancin kasar nan don kawo sauyi mai ma’ana a rayuwar kasar nan.
Sanarwar mai taken: “Kamar tsohuwar zuma, Shugaba Buhari shekarunsa na karuwa ne yana kara inganci,” ta kara da cewa: “A ranar Litinin Shugaba Muhammadu Buhari ya gana da ’yan Najeriya a ofishin jakadancin Najeriya da ke Johannesburg a Afirka ta Kudu. Ya yi magana cikin balaga da fasaha, saboda yana son bayyana wa mutane ‘hakikanin abin da ke zuciyarsa,’ inda Shugaban ya bukaci su kasance jakadun Najeriya nigari kasar da suka yi yaki tare da kasacewarta a dunkule.”
Kakakin Shugaban kasa ya wanda ke karin haske kan kalama Shugaban kasa ya kara da cewa: “Lokacin da yake dada fito da martabar kasarmu Najeriya, Shugaban kasar wanda ya taba zama Gwamnan Soja a Jihar Arewa maso Gabas yana da shekara 33 ya ce ne: “Na so a ce na zama Shugaban kasa (a shekarun) da na zama Gwamna. Amma a yanzu da na shekara 72 abin da zan iya yi takaitacce ne.”
Sanarwar ta kara da cewa: “Wannan bayani da wasu jaridu suka ruwaito ne wasu suka dauka yana nufin ya tsufa tukuf ba zai iya yin aikin da aka zabe shi ya yi ba. Wannan bah aka ba ne. Kamar yadda masu iya magana suke cewa ne; “da tsohuwar zuma ake magani,” don haka Shugaba Buhari da muke da shi yanzu, tamkar tsohuwar zuma ne wadda ta fi sabon yankan rake. A shekarunsa 72 ba za a iya kiransa matashi ba, amma yana da kundin hikima da hakuri da sakakkiyar zuciya da danne zuciya da yawan shekaru ke haifarwa. Kuma dukkan wadannan kyawawan halaye da ya zo gadon mulki da su, za su kawo sauyi nagari a harkokin rayuwar kasar nan. Shugaban kasar ya ba ’yan Najeriya mazauna Afirka ta Kudu tabbacin cewa gwamnatinsa za ta inganta kasar nan.”
Ya kara da cewa: “Rashin tsaro da ake fama da shi sakamakon hare-haren Boko Haram zai kawo karshe, za a yaki cin hanci da rashawa sau da kafa, za a kirkiro ayyukan yi ga dimbin marasa aiki, za a farfado da tattalin arziki, rayuwar ’yan Najeriya ta koma sabuwa. To amma wadannan ba za su zo a dare daya ba, amma insha Allahu za a samu haka a karkashin wannan gwamnati.”
Ya ce “Duk da Buhari yana da shekara 72, halaye da dabi’unsa ba su canja ba. Yana nan mutum mai saukin kai da gaskiya da rikon amana, dan kishin kasa marar almundahana kamar yadda yake a baya. Kuma saboda ’yan Najeriya suna bukatar canji ne suka zabe shi da gagarumar rinjaye a zaben watan Maris na bana. Dukkan dabi’u da halayen Buhari na kirki zai yi amfani da su wajen gudanar da shugabanci nan da ’yan makonni da watanni masu zuwa.” Sanarwar ta kara da cewa, “Al’ummar Najeriya mazauna Afirka ta Kudu sun cika da farin ciki kan kalaman na Shugaban kasa, kuma da kyar ya samu fita daga wurin sakamakon yadda suka kewaye shi kowa yana son ya sha hannu da shi.”
A ranar Talata ce wata kungiyar PDP mai suna PDP Media Watchdog, ta bukaci Buhari ya yi murabus kan wadancan kalamai, inda ta alkanta hakan da cewa ya tsufa.
Shugaban kungiyar Tunde Lawal ya ce: “Mako uku ke nan na fara mulkin Shugaba Muhammadu Buhari yana batun shekarunsa, to me zai faru ga Najeriya a sauran kwana 1,440 na wannan gwamnati? Ya fi dacewa a nema wa tufkar baki tun kafin lokaci ya kure, don haka muke neman Buhari ya yi murabus a yanzu, saboda ’yan Najeriya ba za su lamunci duk wani uzuri nan gaba ba game da dalilin da APC ba za ta iya cika alkawuran da ta yi a kamfe ba.”
Sai dai Jam’iyyar PDP ta nesanta kanta daga wannan kungiya inda Kakakinta Olisa Metuh ya ce: “Wannan kungiya ba sananniya ba ce ga PDP, kuma ba ta da alaka da ita ta kowane gefe a kowane mataki, kuma bayanin da ta yi ba ra’ayinmu ba ne kuma bai dace da matsayin jam’iyya ba. Jam’iyyarmu ba ta umarci wanna kungiya ta yi amfani da sunanta ko tambarinta don bayar da sanarwa ko magana a madadinta kan kowane al’amari ba, kuma muna gargadin wadanda suke daure musu gindi su daina yin haka nan take.”
Jam’iyyar PDP ta nesanta kanta daga abin kunyar da kungiyar ta yin a kiran Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi murabus, tare da amfani da kalaman rashin da’a ga mutumtaka da ofishin Shugaban kasar.
Kakakin Jam’iyyar APC na kasa Alhaji Lai Mohammed ya yi Allah wadai da kalaman na kungiyar, inda ya zargi kungiyar da karancin ilimin harshen Ingilishi. Ya ce, “Abin da Shugaban kasa Buhari ya ce da suka kasa fahimta shi ne, tsananin son da yake yi wa kasar nan ne, ya sa duk da shekarunsa da ya kamata a ce ya yi ritaya, amma ya fito neman shugabancin kasar nan, bayan shekara 30 da mulkarta.” Lai ya kara da cewa: “A shekara 16, ’yan Najeriya sun ba PDP uzuri ta kai kasar nan tudun mun tsira, amma sai jam’iyyar ta mayar da hannun agogo baya, kuma an kauce wa fadawa hallaka ne, ta hanyar korarta daga gadon mulki. Kuma wannan ne ya sa Buhari ya rika takarar neman shugabancin kasar nan ta yadda zai taimaka wajen mayar da kasar kan duga-duganta. Wannan ne kawai, ba wai don ya ji dadin mukamin ba ko shan lagwada. Da an tafiyar da kasar nan yadda ya kamata Buhari mai shekara 72 ba zai zo yana wahalar da kansa wajen zagaya duniya yana nema wa Najeriya mafita ba.”
Jam’iyyar ta APC ta ce, makiya kasa da dimokuradiyya ne kawai za su bukaci Shugaban kasar wanda ko wata daya bai yi a gadon mulki ba, ya yi murabus, inda ta kara da cewa: “Abin takaici ne ganin masu yi wannan kira sun fito ne daga jam’iyyar da ta gaza yin abin kirki a cikin shekara 16.”