✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Buhari Ne Ya Gina Hanyar Garinku, Ya Kori Boko Haram —APC Ga Atiku

Lai Mohammed ya ce sai da Buhari ya zo ne ya gina titin zuwa mahaifar Atiku, wanda ya shekara takwas yana mataimakin shugaban kasa a…

Ministan Yada Labarai Da Raya Al’adu, Lai Mohammed, ya ce gwamnatin APC ce ta kwato mahaifar dan takarar shugaban kasa na PDP, Atiku Abubakar daga hannun ’yan ta’addan Boko Haram.

A martaninsa ga zargin Atiku cewa gwamnatin APC ba ta tabuka komai ba a shekara takwas, Lai Mohammed ya ce, a bangaren ababen more rayuwa sai da Gwamnatin Buhari ta zo sannan ta gina hanyar zuwa mahaifar Atiku, duk kuwa da ya shekara takwas a matsayin mataimakin shugaban kasa.

Bidiyon Dala: Ganduje da Jaafar Jaafar sun hadu a London

NAJERIYA A YAU: Yadda Jirgin Kasan Abuja-Kaduna Ya Dawo Aiki

Lai Mohammed ya ce, “Ko da wani zai soki gwamnatinmu, to Atiku ba shi da ta cewa, domin shekararsa takwas a matsayin mataimkakin shugaban kasa a mulkin PDP na shekara 16, amma mahaifarsa ko titin arziki da mota za ta bi babu, har sai da gwamnatinmu ta zo ta yi.

“Kuma wannan titi na Mayo Belwa- Jada-Ganye-Toungo shi Atikun ke bi yanzu ya je mahaifarsa, Jada.

“Mu koma batun tsaro, kafin zaman Buhari shugaban kasa, a mulkin PDP Boko Haram ta kwace kananan hukumomi biyar da ke Adamawa ta Arewa, mazabar da Atiku ya fito.

“Kungiyar ta fatattaki hukumomin gwamnatin da ofisoshin ’yan sanda da kasuwanni da asibitoci da makarantu da kotuna.

“Haka kuma ta mamaye gidajen limamai da sarakunan gargajiya a matsayin fadarta a kananan hukumomin Madagali, Michika, Mubi ta Arewa, Mubi ta Kudu, Maiha, Hong da kuma Gombi da ke Jihar Adamawa.

“Har wani na hannun daman Atikun Boko Haram ta kashe, amma me ya yi? Daina zuwa jihar ya yi balle ya yi musu ta’aziyya.

“Amma APC ta kawar da duk wadannan abubuwa a yanzu.

“Don haka Atiku ya ja bakinsa ya yi shiru, domin ba shi da abin sukar gwamantin Buhari ko kadan,” in ji Lai.