Shugaban asibitin fadar shugaban kasa, Hussain Munnir ya ce shugaban kasa Muhammadu Buhari na sane da halin da aibitin ke ciki.
Malam Munnir ya ce tun kafin Uwargidan shugaban qasa Aisha Buhari ta koka da yanayin da asibitin ke ciki na rashin kayan aiki, ya aike da kokensa zuwa ga shugaban a kan cewa asibitin na bukatar kayan aiki.
Kafar yada labarai na Premium Times ta ruwaito cewa, Malam Munninr ya aike da saqo zuwa shugaban ma’aikata na fadar shugaban kasa, Abba Kyari a ranar 3 ga watan Oktoban bara, sannan kuma ya rubuta wasu guda biyu kafin nan.
A cikin saqon da ya aika na ranar 3 ga watan Oktoba, abubuwan da ya rubuta a ciki sun hada da batun rashin isasshen kudin da za a saya kananan kayan aiki da suka hada ha magunguna.
Malam Munnir ya nuna cewa a cikin Naira miliyan 290.4 da aka ware wa asibitin domin sayan magunguna a shekarar 2017, Naira miliyan 29 kawai aka kashe.
Hakanan kuma daraktan asibitin ya ce, a cikin Naira biliyan 3.8 da aka ware wa asibitin a shekarar 2016, Naira miliyan 25 kawai aka kashe a kan magunguna, wanda ya yi kasa sosai da kudaden da ake kashewa a shekarun baya.
Malam Munnir dai ya yi wannan karin hasken ne bayan wani rahoto da Jaridar Daily Trust/Aminiya ta buga na yadda majinyata ke kokowa da rashin magunguna a asibitin.