Shugaba Buhari ya aike wa Majalisar Dattawa takardar neman amincewarta ya tabbatar da nadin Mai Shari’a Monica Dongban-Mensem a Matsayin cikakkiyar Shugabar Kotun Daukaka Kara ta Najeriya.
Majalisar ta tabbatar da samun takardar Shugaba Buhari na neman nada Mai Shari’a Dongban-Mensem, wadda ita ce mukaddashin Shugaban Kotun a yanzu.
Shugaban Majalisar Ahmad Lawan ya karanta wasikar Shugaban Kasar a zaman Majalisar na ranar Talata.
“Ina neman yardar Majalisa domain nada Mai Shari’a Monica Dongban-Mensem ta zama Shugabar Kotun Daukaka Kara ta Najeriya, kamar yadda doka ta tanadar.
“Ina fata Majalisa za ta duba tare da amincewa da wannan bukatar a kan kari”, inji wasikar.
A ranar Litinin ne Fadar Shugaban Kasa ta sanar da cewa Buhari na neman ba wa Dongban-Mensem cikakken iko a Kotun.