✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Buhari na neman majalisa ta amince da sabon shugaban Sojin Kasa

Nadin nasa dai ya biyo bayan rasuwar Laftanar Janar Attahiru sakamakon hatsarin jirgin sama.

Majalisar Dattawa ta karbi bukatar Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a hukumance domin amincewa da Manjo Janar Faruk Yahaya a matsayin Babban Hafsan Sojin Kasa.

Bukatar hakan na kunshe ne a cikin wata wasika da shugaban Majalisar, Sanata Ahmed Lawan ya karanta a zauren majalisar ranar Talata.

Buhari dai ya bukaci majalisar da ta duba tare da amincewa da bukatar la’akari da muhimmancinta.

Shugaban dai ya nada Manjo Janar Yahaya ne bayan rasuwar Laftanar Janar Ibrahim Attahiru a watan Mayu sakamakon hatsarin jirgin sama.