✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rikicin Mali: Shugabannin ECOWAS sun kammala taro

Shugabannin kasashen ECOWAS sun yi tattaunawar gaggawa a kan juyi mulki a Mali

Shugaban Kasa Muhammadu da sauran shugabannin kasashen Yammacin Afirka ta Yamma sun kammala tattaunawa a kan rikita-rikitar siyasar kasar Mali.

Taron wanda ya gudana ta fasahar bidiyo ya biyo bayan juyin mulkin da sojoji suka yi ranar Talata a Malin, wanda ECOWAS da sauran kasashen duniya suka la’anta.

Shugaba Buhari ya halarci taro ne daga dakin taro na Fadar Shugaban Kasa tare da Ministan Harkokin Waje, Geoffrey Onyeama, da Minista a Ma’aikatar Harkokin Waje, Ambasada Zubairu Dada da Ministan Tsaro, Manjo Janar Bashir Magashi mai ritaya.

Sauran masu halartan taron sun hada da mai ba shi shawara kan harkokin tsaro, Manjo Janar Babagana Monguno mai ritaya, Babban Daraktan Hukumar Leken Asiri ta Kasa (NIA) Ahmed Rufa’i da Shugaban Ma’aikata Fadar Shugaban Kasa, Farfesa Ibrahim Gambari.

A ranar Talata ne sojojin Mali suka kama tsare da Shugaba Ibrahim Boubacar Keita da Firaminista Boubou Cisse bayan sun hambarar da gwamnatinsu.

Daga bisani Keita ya sanar da murabus dinsa ranar Laraba saboda abin da ya kira ‘kaucewa zubar da jini’ a kasar.

Tuni dai Kungiyar Bunkasa Tattalin Kasashen Afirka ta Yamma ta ECOWAS ta sha alwashin kulle iyakokin ruwa da na kasa na kasashen da ke da iyaka da kasar ta Mali tare da kokarin sanya mata takunkumi don ganin sojojin sun mayar da mulkin ga farar hula.

Kungiyar mai mambobin kasashe 15 ciki har da Malin ta ce za ta dakatar da kasar daga cikinta.

Ko a watan Yuli sai da ECOWAS din ta bayar da shawarar kafa gwamnatin hadin kan kasa don ganin an samu maslaha, amma ‘yan adawa suka ki amincewa da hakan.