Shugaba Muhammadu Buhari ya karbi bakuncin Firai Ministan Gwamnatin Hadin Kan Kasa ta Libya, Abdul Hamid Dbeibeh, a Abuja.
Dbeibeh tare da jami’an Gwamnatinsa sun isa Fadar Shugaban Kasa da ke Abuja da misalin karfe 10.05 na safe, kuma Shugaba Buhari ya karbe su.
- An sauya shugaban tsaron Masallacin Harami bayan yunkurin kashe limami
- Ya yi wa abokinsa yankan rago
- Ina kudaden da aka kwato suke? Sarkin Musulmi ga Gwamnati
Shugaba Buhari da Majalisar Ministocinsa da ma wasu hadiman Fadar ne suka tarbi bakin a fadar gwamnatin.
Ana sa ran shugabannin biyu za su tattauna kan batutuwan da suka shafi kasashensu da nufin kawo cigaba da bunkasa tattalin arzikin kasashen biyu.
Firai Minista Dbeibeh zai yi amfani da damar domin yi wa Buhari da mutanen Najeriya ta’aziyyar rasuwar Babban Hafsan Sojojin Kasa, Laftanar-Janar Ibrahim Attahiru da wasu hafsoshin soja 10 a ranar Juma’ar da ta gabata.
A ranar Talata, shugaban na Libya ya halarci Babban Taron Shugabannin Kasashe da Gwamnatocin Hukumar Tafkin Chadi (LCBC), wanda aka gudanar a Abuja.