✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buhari da Muslim

Tare da Sheikh Yunus Is’hak Almashgool, Bauchi Babi na Ashirin da Uku: Wanda ya nemi haihuwa don dan ya zamo mayakin daukaka kalmar Allah: 509. An…

Tare da Sheikh Yunus Is’hak Almashgool, Bauchi

Babi na Ashirin da Uku: Wanda ya nemi haihuwa don dan ya zamo mayakin daukaka kalmar Allah:

509. An karbo daga Laisu ya ce: “Ja’afar dan Rabi’ata ya ba mu labari daga Abdurrahman dan Hurmuz ya ce: “Na ji Abu Huraira (RA) ya ce, daga Manzon Allah (SAW) ya ce: “Sulaiman dan Dauda (AS) ya ce: “Lallai zan tara da matana dari duk a cikin wannan dare ko dari tara da casa’in, ina fatar ko dukansu za su haifi gwarzon mayaki domin daukaka kalmar Allah. Sai abokinsa ya ce masa, “Ka ce in Allah Ya so, bai ce in Allah Ya so ba. Babu wadda ta samu ciki daga matan face mace daya, kuma dan ya kasance rabin mutum shanyayye.” Ya ce: “Ina rantsuwa da wanda ran Muhammad ke hannunSa da ya ce, in Allah Ya so, da sun haifi wadanda za su yi yakin domin daukaka kalmar Allah kuma za su zama gwarzaye dukansu.”

 

Babi na Ashirin da Hudu: Magana a kan jaruntaka da tsoro a fagen yaki:

510. An karbo daga Ahmad dan Abdulmalik dan Wakid ya ce: “Hammad dan Zaid ya ba mu labari daga Sabit daga Anas (Allah Ya yarda da shi), ya ce: “Annabi (SAW) ya kasance ya fi mutane kyautatawa, kuma ya fi kowa jaruntaka. Kuma ya fi kowa alheri, domin akwai ranar da mutanen Madina suka firgita, Annabi (SAW) ya riga su bincikar abin da ya faru bisa wata godiya ya ce: “Mun samu wannan godiya da gudu kamar ruwan kogi.”

511. An karbo daga Abul Yaman ya ce: “Shu’aib ya ba mu labari daga Zuhuri ya ce, Umar dan Muhammad dan Jubair dan Mud’im ya ba ni labari cewa: “Lallai Muhammad dan Jubair ya ce, Jubair dan Mud’im ya ba ni labari ya ce: “Wata rana suna tafi tare da Manzon Allah (SAW) mutane na tare da shi lokacin da ke komowa daga Hunain. Sai wadansu (Larabawan kauye) suka rika rokonsa bisa wata bukatarsu har suka sanya ya fada cikin itacen kayoyi Samura rigarsa ta makale. Annabi (SAW) ya tsaya ya ce: “Ku ba ni riga ta (mayafina)! Da a ce zan mallaki taguwa misalin yawan wannan kayoyi da na raba su gare ku. Ba za ku same ni marowaci ba, kuma ba za ku same ni makaryaci ba, kuma ba za ku taba samuna matsora ci ba.”

  

Babi na Ashirin da Biyar:  Abin da ake neman tsari da shi daga tsoro:

512. An karbo daga Musa dan Isma’il ya ce: “Abu Awana ya ba mu labari ya ce, Abdulmalik dan Umair ya ce: “Na ji Amru dan Maimun Audi ya ce: “Sa’ad ya kasance yana karantar da ’ya’yansa wadannan kalmomi, kamar yadda malami ke koyar da yara rubutu. Kuma yana cewa: “Hakika Manzon Allah (SAW) ya kasance yana neman tsari da su (wadannan kalmomi) a karshen kowace Sallah: “Allahumma Inni a’uzubika minal jubni. Wa a’uzubika an uradda ila arzalil umuri. Wa a’uzubika min fitnatid dunya. Wa a’uzubika min azabil kabri.” Sai ya bayar da labarin haka ga Mus’ab ya gaskata shi.

513. An karbo daga Musaddad ya ce: “Mu’atamir ya ba mu labari ya ce, na ji Babana ya ce, na ji Anas dan Malik (RA) ya ce: “Annabi (SAW) ya kasance yana cewa: “Allahumma inni a’uzubika minal ajzi wal kasali, wal jubni, wal harami. Wa a’uzubika min fitanatil mahya wal mamati. Wa a’uzubika min azabil kabri (Ya Allah! Ina neman tsari daga gazawa da ragwanci, kuma ina neman tsarinKa daga tsoro da tsufa. Ina neman tsarinKa daga fitinar rayuwa da mutuwa, ina neman tsarinKa daga azabar kabari).”