Kungiyar Gwamonin Najeriya (NGF) tare da Shugaban Buhari na ganawa da manyan hafsoshin tsaro kan matsalolin tsaro a kasa.
Ganawar sirri da Majalisar Tsaro ta Kungiyar Gwamnonin na zuwa ne bayan gwamnonin yankin Arewa ta Gabas sun yi makamanciyarta da Shugaban Kasar da shugabannin tsaro na Kasa a ranar Litinin.
Taron sirrin ya samu halarcin Mataimakin Shagaban Kasa da dukkanin manayan hafshoshin tsaro da shugabannin hukumomin tsaro.
Kazalika Ministan Tsaro Bashir Magashi da Mai ba da Shawara kan Tsaron Kasa Babagana Monguno da Sakataren Gwamnatin Tarayya Boss Mustapha da kuma Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa Ibrahim Gambari suna cikin mahalarta.
Shugaban Majalisar Tsaro ta Kungiyar Gwamnoni, Gwamna Yahaya Bello shi ma ya halarci taron tare da takwarorinsa na jihohin Bayelsa, Senator Douye Diri da Borno, Babagana Zulum da Ebonyi, David Umahi, da kuma gwamnan Legas, Babajide Sanwo-Olu.