Majalisar Dattawa ta tabbatar da cewa zaman Shugaba Muhammadu Buhari a birnin Landan na fiye da kwanaki 90 yana jinya bai saba dokar kasa ba kamar yadda wasu ke yadawa.
A dai cikin makon nan ne wasu kungiyoyin al’umma suka gudanar da zanga-zanga a babban birnin tarayya Abuja dauka da alluna daban-daban, inda suke kira ga Shugaban Kasar, Muhammadu Buhari da dawo bakin aiki ko kuma ya sauka.
A wata sanawar da shugaban kwamitin yada labarai na Majalisar Dattawar, Sanata Aliyu Sabi Abdullahi ya bayyana cewa Buhari ya mutunta tanadin tsarin mulkin kasar nan wanda aka yi kwaskwarima a shekarar 1999, wadda ya bukaci da ya mika ragamar mulki ga mataimakinsa tare kuma da sanar da majalisar tarayya, kamar yadda ya aiwatar.
Haka zalika Sanata Abdullahi ya bukaci masu zanga-zangar neman Shugaba Buhari ya yi murabus kan su dakatar da yin hakan, saboda majalisar tarayya ta gamsu da irin jagorancin Mukaddashin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo.