✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buhari bai damu da matsalar tsaro kamar COVID-19 ba —Bafarawa

Da a sayi maganin rigakafin N400bn gara a yi amfani da su a bangaren tsaro

Tsohon Gwamnan Jihar Sakkwato Attahiru Bafarawa ya koka cewa Shugaba Buhari ya fi damuwa da COVID-19 fiye da matsalar tsaro da ke addabar Najeriya.

Ya bayyana takaici cewa duk da mutum dubu dari hudu da suka salwanta ta dalilin matsalolin tsaro, amman Gwamnatin Buhari ta fi damuwa da COVID-19 wadda ta yi ajalin mutum 2,000, har take neman kashe Naira biliyan 400 wurin sayen maganin rigakafi.

“COVID-19 ba ta kashe yawan mutanen da suka mutu sakamakon rashin tsaro ba. Rashin tsaro ya ritsa da rayuka da dukiyoyi. Da irin hadarin da muke fuskata na rashin tsaro, amfani da N400bn din wurin samar da tsaro zai taimaka matuka wajen saukaka matsalar,” inji shi.

Bafarawa ya ce jama’ar Arewa da ma daukacin ’yan Najeriya na jin haushin gwamnatin Buhari kan yadda sha’anin tsaro ya tabarbace a Najeriya.

Ya ce yayin da sha’anin tsaro ke kara tabarbarewa, maimakon kashe Naira biliyan 400 da gwamnati ta ware a don sayen rigakafin COVID-19, kamata ya yi ta yi amfani da kudaden a bangaren tsaro.

“Ina fadin ahaka ne domin rashin tsaro shi ne coronavirus din Najeriya. COVID -19 ba ta yi yawa a Najeiya ba. Ba amfanin yi wa mutane rigakafi daga baya kuma rashin tsaro ko yunwa su hallaka su? Ko da COVID-19 za mu iya ci gaba da rayuwa” inji Bafarawa.

Ya ce tilas ne Buhari ya karkatar da hankalin gwamnatinsa zuwa ga magance matsalar tsaro fiye da yadda ta tattara hankalinta ya koma kan COVID-19.

A yi mana bayanin kudin da aka kashe

Tsohon gwamnan ya kuma kalubalanci Kwamintin Yaki da COVID-19 na Kasa (PTF) ya bayar da bayan N3.5bn da ya kashe a kan aikinsa.

Ya ce, “Mutanen Najeriya na so sanin yadda aka kashe N3.5bn din ba kawai a yi ta amabaton yawan kudade ba, muna son a ba mu bayani dalla-dalla kan yadda aka yi da kudaden.”

Ya kuma shawarci da ta wayar da kan jama’a tun kafin ta kawo rigakafin COIVID-19, saboda a cewarsa, kashi 60% na zargin lauje cikin nadi a game da kwayar cutar.

“Idan na ga kuskure sai na yi magana, saboda kar wasu sassan kasar nan ya yi tunanin cewa muna jin dadi ko goyon bayan abin da bai dace ba.

“Amma gaskiyar lamari shi ne mu ’yan Arewa ba ma jin dadin abin da ke faruwa.

“A wurina Najeriya daya ce, babu batun son zuciya, muna magana ne a madadin mutanen da ba a jin muryoyinsu kuma na tabbata matsalar ta dami yawancin ’yan Najeriya.

“Kwana biyu da suka wuce an kashe mutum 14 a kauyenmu, kuma har yanzu ba abin da ya karu game da sha’anin tsaro,” inji shi.

Matsalar tsaro ta dame mu

Gwamnatin Tarayya ta sha nanata aniyarta ta kawo karshen matsalar tsaron da ta addabi kasar.

A lokuta ta dama gwamantin ta kafa rundunoni na musamman domin magance matsalolin tsaro a sassan Najeriya.

Gwamnatin ta kuma kashe biliyoyin Naira a kan harkar tsaro da niyyar ganin bayan matsalolin da ke addabar kasar.