✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buhari ba zai hana ni takara ba – Ali Ndume

Daya daga cikin masu takarar  Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Mohammed Ali Ndume ya ce yana tunanin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ba zai tursasa shi ya…

Daya daga cikin masu takarar  Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Mohammed Ali Ndume ya ce yana tunanin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ba zai tursasa shi ya janye wa wani dan takara ba.

Sanata Ndume ya ce Shugaba Buhari mutum ne da ya yarda da tsarin dimokuradiyya, don haka ba zai sanya baki ba a harkar zaben shugabannin majalisa.

Sanata Ali Ndume ya bayyana haka ne lokacin da yake zantawa da Editocin Kamfanin Media Trust masi buga jaridun Daily Trust da Aminiya lokacin ziyararsa Hedkwatar Kamfanin a Abuja shekaranjiya Laraba, inda ya ce shi ma ba ya so kowane dan takara ya janye masa. “Mu ’yan Majalisar Dattawa ne, don haka bai kamata wani ya zaba wa dattawa shugaba ba. Kamata ya yi a bar su su zabi shugaban da suke so,” inji shi.

Ya ce, “Ba na tunanin Shugaba Buhai zai ce in janye wa wani dan takara domin bai taba shiga harkar zaben wani ba. Kuma ban ga dalilin da zan janye ba.

“Kawai mu yi zabe, sanatoci su zabi wanda suke so. Ba na so a yi mana dauki-dora, domin shi kansa Shugaban Jam’iyyar APC din ba dauki-daura aka yi ba. Don haka ba na tunanin wani zai sani in janye,” inji shi.

“A lokacin da Shugaba Buhari ya yi takara ta farko, akwai ’yan takara irin su Kwankwaso da Okorocha da Sam Nda-Isiah da sauransu. Okorocha ya tsaya takara a lokacin duk da cewa an ce dan Arewa ake so.”

Ndume ya ce, “Maganar gaskiya ita ce ba na bukatar kowa ya janye min. ko a zaben fid da gwani an bukaci a janye min, sai na ce a’a, a bari kawai a yi zabe. Amma ’yan takara suna iya zama a tsakaninsu su fitar da mutum daya.”

Game da alakar da ke tsakaninsa da sauran ’yan takara, Sanata Ahmed Lawan da Sanata Danjuma Goje, ya ce, “Muna zaman lafiya da su. Muna mu’amala kamar ’yan uwa. Ina da tabbacin dukansu suna da gudunmawar da su iya bayarwa.”

Kan ko Jam’iyyar APC ta yi kuskure wajen tsayar da Ahmed Lawan a matsayin dan takara, sai ya ce, “Ba na tunanin Jam’iyyar APC ta fitar da mutum daya, ballantana in ce ta yi kuskure. Oshiomhole Shugaban Jam’iyya ne ya bayyana haka, ba jam’iyya ba . Shugaban Kasa bai nuna yana tare da matsayar ba. Amma shi Oshiomhole ya yi kuskure wajen fitar da mutum daya. Amma wanan ra’ayinsa ne, ba zai shafe ni ba.”

“Na rubuta wasika zuwa ga jam’iyya cewa zan nemi kujerar, amma sauran ’yan takarar ba su yi ba. Don haka abin da Oshiomhole yake yi ya saba kundin tsarin jam’iyya, ni kuma ina bin kundin tsarin jam’iyya ne,” inji shi

Ndume ya ce daya daga cikin dalilan da suka sa suka bukaci a ba Arewa maso Gabas Shugaban Majalisar Dattawa shi ne yadda yankin yake fama da matsalolin tsaro.