✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Buhari ba shi da alhakin magance matsalar tsaro —Isa Yuguda

Duk wani abu da ke faruwa ba daidai ba ta fuskar tsaro, to wannan alhaki ne na Gwamna.

Tsohon Gwamnan Jihar Bauchi, Isa Yuguda, ya ce Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ba shi da alhakin tsare rayuka da dukiyoyin al’umma a kasar nan.

Malam Yuguda, wanda kuma tsohon Ministan Sufurin Jiragen Sama ne, ya yi wannan tsokaci ne a wani shirin karin kumallo na gidan talabijin din Channels, Sunrise Daily a ranar Litinin.

Isa Yuguda ya yi tsokacin ne yayin da yake jaddada cewa Buhari ya yi iya bakin kokarinsa wajen tafiyar da al’amuran kasar nan duk da matsalolin tsaro da tattalin arziki da ake fuskanta.

“Tabbas Shugaban Kasa [Buhari] ya yi iya kokarinsa, duk da cewa kokarin kowa ya bambanta, amma zan iya cewa Buhari ya yi iya nasa kokarin.

“Kuma ya [Buhari] nada hadimai da za su taimaka masa wajen tafiyar da kasar – su ma suna yin iya kokarinsu.

“Duk dai wannan ya dogara ne a kan nazarin da auna kwazon da kowa ya yi, kuma ni a nawa ganin, Shugaban Kasa ya yi iya nasa kokarin.”

Yayin da aka nemi jin ta bakinsa, tsohon gwamnan ya yarda cewa alkaluman sha’anin tsaro da tattalin arziki kasar “wani babban abu ne mai matukar takaici da damuwa,” sai dai ya nanata cewa ba laifin shugaban kasar ba ne.

“Duk wani dan Najeriya mai hangen nesa da sanin ya kamata, ya san cewa babu wani bambanci da za a samu ko da wani daban ne yake shugabantar Najeriya ba Buhari ba.

“Galibin abubuwan da ke faruwa damu a halin yanzu tarihi ne yake maimaita kansa.

“Duk yadda ta kasance an assasa tubali marar inganci kan kowane irin al’amari, babu yadda za a yi a samu sakamako mai nagarta.. don haka duk abinda aka shuka shi za a girba.

“Alal misali, matsalar sha’anin tsaro, abu ne da ya faru a tarihi. Ba gwamnatin Buhari ba ce farau domin kuwa ta faru a shekarar 2008 da 2009.

Yuguda ya kara da cewa, ba za a iya danganta kalubalen tsaro da Buhari ba duk da kasancewarsa shugaban kasa.

“Eh, shi ne shugaban kasa baki daya, amma idan ka ga wani abu na faruwa ba daidai ba ta fuskar tsaro, to wannan alhaki ne na Gwamna..

“Duk wani gwamna sai da ya karbi rantsuwar kare rayuka da dukiyoyi al’ummar jiharsa kuma kowacce jiha an yi mata iyaka da ’yar uwarta.

“Shugaban kasa ba shi da wata jiha da aka dora wa alhakin tsare rayuka da dukiyar al’ummar cikinta, saboda haka bai kamata a rika tsamannin shugaban kasa zai yi aikin da rataya a wuyan kowane gwamna ba.”