Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bayyana goyon bayansa ga shugabancin Victor Giadom a matsayin shugaban riko na jam’iyyar APC na kasar.
Babban Mai ba Shugaban Kasa Shawara kan Yada Labarai Garba Shehu ya sanar da cewa Buhari zai halarci taron Majalisar Zartarwar Jam’iyyar APC na kasa da shugabancin Giadom ya kira, kuma ana sa ran gwamnonin jam’iyyar ma za su halarci taro na ranar Alhamis.
Matsayin Buhari ya saba da na uwar jam’iyyar wadda ta dakatar da Giadom, bayan ta nada Abiola Ajimobi a matsayin shugabanta na riko, biyo bayan dakatarwar da Kotun Daukaka Kara ta yi wa Shugaban Jam’aiyyar na Kasa Adams Oshiomhole.
- Yadda Shugaba Buhari ya rage wa gwamnoni karfi
- Rikicin shugabanci: ’Yan sanda sun rufe hedikwatar APC
- Buhari na sane da taron da na kira, inji Giadom
Bayan dakatar da Oshiomhole, Giadom wanda shi ne tsohon Mataimakin Sakataren Jam’iyyar na kas ya garzaya kotu inda ya samo izinin ci gaba da jan ragamar jam’iyyar a bayan Oshiomhole.
Ya kuma sanar da soke zaben fitar da dan takarar gwamnan jam’iyyar na jihar Edo da na Ribas da aka shirya, yana mai cewa zai gudanar da sabo.
A hannu guda kuma uwar jam’iyyar ta ayyana Hilliard Eta a matsayin Mukaddashin Ajimobi wanda ke fama da rashin lafiya, sannan ta dakatar da Giadom, wanda daga baya wata kotu ta dakatar daga jam’iyyar. Kazalika ta ci gaba da zabukan ‘yan takarar da ta shirya gudanarwa a baya.
A ranar Laraba Giadom ya kira taron Kwamitin Zartarwa na Kasan da shugaba Buhari zai halarta, inda a cikin sanarwar Giadom ya bayyana dakatarwar da aka yi masa a matsayin abin dariya. A cewarsa taron shi ne kadai mafita ga rikicin da da ya dabaibaye jam’iyyar.
A bangare guda kuma shugabancin Eta, har ya nada Worgu Boms a gurbin Giadom na Mataimakin Sakataren Jam’iyya daga Jihar Ribas. Eta ya kuma ce Giadom ba dan jam’iyyar ba ne don haka ba shi da hurumin shiga harkokinta balle ya kira taro.
Rikicin jam’iyyar APC ya yi sanadiyyar Babban Sufetan ‘Yan Sandan Najeriya Mohammed Adamu bayar da umarnin rufe hedikwatar jam’iyyar na kasa nan take a ranar Larabar.