Sarkin Musulmi, ya bukaci Shugaba Buhari da gwamnoni su kara daura damara domin shawo kan matsalar tsaron da ake fama da ita a Najeriya.
Sarkin Musulmi Muhammad Sa’ad Abubakar III ya yi kiran ne a sakonsa na barka da sallah ga al’ummar Najeriya bayan azumin Ramadan.
- An kara kona ofishin ’yan sanda a Abiya
- Yahudawa sun raba wa Fulani abincin Sallah
- Dalilinmu na Sallar Idi ran Laraba —Dahiru Bauchi
- Wasu ’yan Izala sun bijire wa Sarkin Musulmi, sun yi Idi ran Laraba
“Shugaban kasa a kara daura damara kan matsalar tsaro, abin da ’yan ta’adda ke yi ba Musulunci ba ne, in su musulmai ne su ji tsoron Allah su daina,” inji sakon da ya gabatar a fadarsa da ke Sakkwato.
Ya kuma yaba wa malamai kan gudanar da tafsiri a bana cikin lumana da kiyaye sharuddan addini, inda suka karantar da mutane tsantsar ilmi , wanda ya ce abin yabawa ne.
Sarkin ya nemi gwamnatin Sakkwato ta kara yi wa jama’a aiki domin karin samun cigaba a fannin noma da kiyon lafiya.
Ya yi wa musulmai barka da sallah da fatan sake ganin wata shekara cikin koshin lafiya.