✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnan Edo makaryaci ne —Ministar Kudi

Ministar Kudi ta karyata zargin buga N60bn kuma ta ce bashin da ake bin Najeriya bai wuce kima ba

Gwamnatin Tarayya ta karyata Gwamnan Edo, Godwin Obaseki wnda ya ce sai da ta buga karin Naira biliyan 60 sannan aka iya raba wa jihohi kudade a watan Maris.

Ministar Kudi, Zainab Ahmad ta ce karya ce tsagwaro Obasekin ya fada wa taron masu ruwa da tsaki na Jihar Edo a ranar Asabar cewa kudaden da yake cewa an buga ne aka raba wa jihohi.

Obaseki ya shaida wa taron cewa “Da muka je taron Kwamitin Rabon Kudaden Gwamnati (FAAC), sai da Gwamnatin Tarayya ta buga karin Naira biliyan 50 zuwa 60 domin cike gurbin abin da za mu raba.

“A watan Afrilu kuma za mu je Abuja a raba. Zuwa karshen shekarar nan dai bashinmu zai iya kaiwa tsakanin Naira tiriliyan 15 da tiriliyan 16,”

Tsabar karya ce —Minista

Amma Ministar kudin ta ce kudaden harajin da ake tarawa a cikin gida kuma ne ake rabawa a FAAC kuam ana iya samun bayanansu a shafin Ma’aikatar Kudi ta Tarayya.

Ta shaida wa manema labarai a Fadar Shugaban Kasa cewa, “Maganar ta Gwamnan Edo abin takaici ne saboda ba gaskiya ya fada ba. Kudaden da muka raba a FAAC haraji ne da aka tara kuma bayanansu na shafin hukumar, kowa zai iya gani.

“Mun bayyana abin da kowanne daga cikin FIRS, Kwastam da NNPC suka tara aka kuma raba a FAAC. Saboda haka karya yake yi cewa mun buga kudi an raba a  FAAC, karya ce”.

“Bashinmu bai wuce kima ba”

Ministar ta kuma yi fatali da zargin da Obasake ya yi cewa bashin da ke kan Najeriya ya wuce misali, inda ta ce har yanzu kasar ba ta ci bashin da ya fi karfinta ba.

“Maganar bashi kuma, har yanzu bashin kasar bai wuce kima ba. Abin da ya kamace mu yi dai shi ne mu fadada hanyoyin da za mu biya basukan da kumasamar da kudaden gudanar da gwamnati na yau da kullum.

“Saboda haka bashinmu na kashi 23% na kayan da ake samarwa a cikin gida abu ne da ba zai gagare mu ba. Rahoton cibiyoyin kasashen duniya na nan za ku iya gani,” a cewarta.