✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Budurwa ta sace motar saurayinta a Kano 

Bayan saurayin ya je sayi mata Shawarma ta yi awon gaba da motarsa

An kama wata budurwa da ta sace motar saurayinta ta gudu bayan ya fita sayo mata Shawarma a unguwar Kofar Famfo, da ke kan titin Jami’ar Bayero a Birnin Kano.

Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya tabbatar wa manema labarai cewa wanda aka dauke wa motar a ranar 12 ga Yulin 2022,  ya kai korafin cewa an sace masa mota.

Bayan da ’yan sandan sun kama ta, budurwar mai suna Ilham, ta bayyana cewa tana bin saurayin nata kudi ne N150,000 kuma tana ganin ba zai ba ta ba, shi ya sa ta yanke shawarar dauke masa mota.

Sai dai a cewar saurayin, sun yi waya ne kuma suka hadu a hauren wanki, inda daga nan ta ce tana jin yunwa kuma Shawarma take son ci.

Sai dai fitarsa ke da wuya domin siyo wa ya dawo ya tarar da motar ta yi batan-dabo.

Ilham dai ta bayyana wa ’yan sanda cewa wani saurayinta ta kirawo ya tuka motar ya tafi da ita gida ya ajiye mata kuma ta dauki motar ne domin kudin da take bin saurayin.

Tuni dai aka kama ta da saurayin nata da ya tuka motar domin ci gaba da bincike.