Wata budurwa ta roki kotun shari’ar Musulunci da ke Rigasa Kaduna ta karbo mata N180,000 da ta ranta wa tsohon saurayinta ya ki biyan ta.
Yayin zaman kotun, budurwar ta ce ta ranta wa masoyin nata N230,000 domin gayara motarsa, amma har suka rabu N50,000 kacal ya biya ta.
- Arewacin Najeriya Zai Kasance A Yanayin Hazo Na Kwana 3 —NIMET
- An Kama Mata Masu Sayen Katinan Zabe a Kano
Ta ce duk kokarin da ta yi don ya biya ta sauran kudi ya ci tura, don haka ta shigar da kara.
A nasa bangaren saurayin ya ce lokacin da ta ba shi kudin, ba ta fada masa bashi ne ba.
“Duk loakcin da ta ganni cikin damuwa, ta kan tambaye ni har ta ba ni kudi; Amma tunda yanzu ta ce bashi ne, zan dinga biya nta da N20,000 duk wata.”
Daga nan ne alkalin kotun, Abubakar Salihu Tureta, ya yanke N30,000 a matsayin kudin da saurayin zai dinga biya duk wata, farawa daga watan Janairun 2023.