Wata budurwa mai kimanin shekara 17 da haihuwa mai suna Sadiya Usman da ke garin Da’u a karamar hukumar Warawan jihar Kano ta rataye kanta.
Lamarin dai ya faru ne ranar Laraba.
- Dalibin SS 1 ya rataye kansa saboda faduwa jarrabawa
- Rasha za ta iya kai wa makwabtanta hari idan ta yi nasara a kan Ukraine – NATO
Sai dai a cewar mahaifin budurwar, Malam Usman, sabanin zargin da ake yi cewa auren dole ne ya sa ta kashe kanta, ya ce iskokanta ne suka sanya ta aikata hakan.
Mahaifin ya ce, “Yarinyar nan ta dade tana fama da iskokai, don haka nake zargin su suka sanya ta ta aikata hakan amma babu wani batun auren dole da ya sa ta aikata hakan.
“Tana fama da aljanu, domin a wasu lokutan ma suna bugar da ita. Wani lokacin kuma za ka ga ta tashi ranta a bace,” inji shi.
Malam Usman ya ce babu wani batun yi wa yarinyar aure ballantana ma har ta kashe kanta saboda shi.
“To ni a iya sanina ban san yarinyar tana da wani saurayi ba ballantana a yi zargin wannan magana.
“Abin da yake kara tabbatar maka da cewa wannan magana karya ce ana ta yada cewa wai kanin mahaifinta ne zai yi mata auren dole. To ni nine mahaifinta ba ni kuma da wani kani,” inji shi.
Tuni dai Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano ta bakin Kakakinta, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ta bayyana cewa tana nan tana gudanar da bincike a kan lamarin.
A cewar Kiyawa, “Tun da lamarin ya faru muka sami kiran gaggawa daga garin na Da’u, don haka Mukaddashin Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar, Abubakar Zubairu ya bayar da umarni inda jami’anmu suka je wurin suka iske gawarta a rataye. Haka kuma ta yi amfani da turmi guda biyu da mayafi da dankwalinta wajen rataye kan nata.
“Daga nan suka dauki gawar suka kai Babban Asibirin Wudil, inda likita ya tabbatar da rasuwarta,” a cewar Kakakin ’yan sandan.