✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Budurwa ta koma ga iyayenta bayan wata 10 da sace ta

Wata budurwa mai shekara 15 da ake zargin an sace ta a watan Oktoban bara, ta koma gidansu da ke yankin Saburi-Dedei, a Birnin Tarayya…

Wata budurwa mai shekara 15 da ake zargin an sace ta a watan Oktoban bara, ta koma gidansu da ke yankin Saburi-Dedei, a Birnin Tarayya Abuja. Yarinyar wanda aka sakaye sunanta, iyayenta sun sanar da bacewarta ne tun tana ’yar shekara 14 ga ofishin ’yan sanda na Gwagwa, Abuja, kamar yadda jami’ar shigar da kara ta Ma’aikatar Shari’a ta Tarayya Misis Dabid Kafanchan ta sanar da wata kotun majistare da ke garin Jiwa, Abuja, a ranar Lititinin da ta gabata, lokacin da aka gurfanar da wata mata da ake zargi da sace ta. Jami’ar ta ce ’yan sanda sun gano inda matar ke zaune a garin Mpape, Abuja suka kama ta, bayan yarinyar ta dawo gidansu a ranar 8 ga Agusta, inda ta sanar da iyayenta halin da ta samu kanta a yayin zamanta a wurin wadda ake zargin tare da kwayenta biyu. Da ta ke amsa tambayar kotun, wadda ake zargin mai suna Chioma Benjamin, ta amince da aikata laifin da ake yi mata, sai dai ta musanta cewa ta sace ta ne. Ta ce ta dauki yarinyar ne zuwa inda take a matsayin taimako bayan ta yi mata korafin cewa iyayenta sun kore ta daga gidansu, kuma ta ba ta damar ziyartan iyayen a yanzu.  Daga nan ne jami’ar ta nemi kotun ta sassauta hukunci a kan wadda ake zargin saboda ba ta jawo tsaiko ga bincike ba. Mai shari’a Omolola Tolulope ta ba da belinta a kan Naira dubu 50 tare da gabatar da mutum biyu da za su tsaya mata wadanda dole ne su kasance mazauna yankin da kotun ke da hurumi, kuma ta dage shari’ar zuwa ranar 28 ga watan Satumban nan.