Wata budurwa mai kimanin shekara 17 a duniya mazauniyar unguwar Shekar Maidaki da ke Karamar Hukumar Kumbotso a Jihar Kano ta kashe wata makwabciyarta ta hanyar daba mata wuka.
Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya sanar da haka lokacin da yake gabatar da wacce ake zargin ga ’yan jarida a Kano ranar Asabar.
- An kashe mutum 12, wasu da dama sun bace a kauyen Katsina
- ’Yan bindiga sun sako daliban makarantar Bethel 15 a Kaduna
Ya ce tuni rundunar ta kama wacce ake zargin da kashe wata mai suna Bahijja Abubakar mai kimanin shekara 28.
Kiyawa ya ce wacce ake zargin ta daba wa Bahijja wukar ne a wuyanta, lamarin da ya barta cikin jini.
“An kai ta asibiti, amma daga bisani ta ce ga garinku nan,” inji kakakin.
Ya kuma ce jami’an rundunar sun yi aiki da umarnin Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar, CP Sama’ila Shu’aibu Dikko ne lokacin da labarin aikata ta’a sar ya iske shi.
Kakakin ya ce jami’ansu da ke Karamar Hukumar ta Kumbotso, karkashin Baturen ’Yan Sandan Yankin, SP Mudassir Ibrahim ne suka kama wacce ake zargin a wani waje da ta buya a unguwar Zawachiki da ke Kumbotson.
Ya ce jim kadan da samun rahoton ne Kwamishinan ya ba da umarnin a shiga farautar wacce ake zargin.
“Cikin sa’o’i 24, jami’anmu suka isa wajen sannan suka kama wacce ake zargin, yayin da ita kuma marigayiyar aka garzaya da ita Asibitin Kwararru na Murtala Muhammad da ke Kano, sai dai Bahijja ta rasu da misalin karfe 8:00 na safiyar Asabar lokacin da ake ba ta kulawa.
“Mun sami nasarar kama wacce ake zargin, wacce ita ma a unguwar take zaune a dai wannan ranar, da misalin karfe 10:00 na safe a inda ta buya,” injin Kiyawa.
Rahotanni dai sun ce wacce ake zargin ta amince da aikata laifin lokacin da ake yi mata titsiye.
Ta ce wata sa-in-sa ce ta shiga tsakaninsu wacce ta kai ga takaddama, daga bisani kuma fada ya barke.
Wani ganau a ainihin inda fadan ya faru ya ce an sami nasarar raba su a lokacin, amma daga bisani wacce ake zargin ta dauko wata wuka mai kaifi ta daba wa marigayiyar, lamarin da ya yi sanadin mutuwarta.