An tsinci gawar wata budurwa ’yar shekara 18 mai suna Waliyah a wata rijiya a Jihar Kwara.
Wannan dai na zuwa ne kasa da sa’o’i 24 bayan an gano gawar wani yaro dan shekara bakwai bayan ya zame ya fada cikin rijiya a yankin Akerebiata, Karamar Hukumar Ilọrin ta Gabas a Jihar Kwara.
- Gas din girki ya kara tashin gwauron zabo a Kano da Legas
- Za mu dauki mataki kan wadanda suka kai wa alkali hari a Gombe —Lauyoyi
Lamarin na baya-bayan nan ya faru ne da misalin karfe 6:46 na yammacin ranar Talata a Ile-Olodo, unguwar Ita Merin a Karamar Hukumar Ilorin ta Yamma.
Wakilinmu ya samu labarin cewa, faduwar matashiyar a cikin rijiyar ya firgita wasu mazauna unguwar.
Kakakin hukumar kashe gobara ta jihar, Hassan Hakeem Adekunle ya ce an mika gawar matashiyar ga Magajin Ile-Olodo, Alhaji Adisa Akanbi.
A cewarsa, “Daraktan hukumar kashe gobara na Jihar Kwara, Prince Falade John, ya gargadi iyaye da su guji sa yaransu debo ruwa a rijiyoyi marasa murfi.”
Kazalika, ya ce sun dauko gawar wani mutum da ya mutu a rijiya bayan an sanar da hukumar game da faruwar lamarin da misalin karfe 5:08 na yammacin ranar Talata.
“Marigayin yana da kimanin shekara 43 kuma an mika gawarsa ga ’yan sanda a Ilọrin,” in ji shi.