✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Budurwa ta banka wa kawarta wuta kan sabani

Matashiyar ta zuwa wa kawarta fetur sannan ta cinna mata wuta.

Wata budurwa mai shekara 16 ta gurfana a gaban kotu a ranar Talata kan banka wa abokiyar aikinta wuta da ta yi saboda wani sabani da suka samu.

Budurwar wadda aka sakaya sunanta bulbula wa abokiyar tata mai suna Fatimoh Jako wuta ne a garin Moshegada da ke Karamar Hukumar Kaiama ta Jihar Kwara.

Bayan ta yi aika-aikan ne jami’an tsaro suka cafke ta suka tisa keyarta zuwa Sashen Binciken Manyan Laifuka na Rundunar ’Yan Sandan Jihar da ke Ilorin, babban birnin Jihar.

’Yan matan biyu sun kasance suna koyon aiki ne a wani shagon sayar da magunguna, amma sabanin da ke tsakaninsu ya sanya aka mayar da ita zuwa wani shagon.

Binciken ’yan sanda ya gano cewa bayan haka ne wadda ake zargin ta samo man fetur, sannan ta saci jiki ta shige dakin Fatimoh a lokacin da take barci, ta zuba mata man ta kuma cinna mata wuta.

An yi kokarin ceto rayuwar Fatimah, inda aka garzaya da ita zuwa Asibitin Koyarwa na Jami’ar Ilorin (UITH), amma a can rai ya yi halinsa.

Yayin bincike, matashiyar ta amsa wa ’yan sanda cewa aikata laifin, ta kuma tabbatar musu cewa wani sabani ne da ya faru tsakaninsu ne ya sa ta yi aika-aikan.

Alkalin Kotun Majistaren da ke zamanta a Ilorin, F.O Olokoyo ya dage sauraren shari’ar zuwa ranar 30 ga watan Agusta, 2021 saboda rashin hurumin sauraron karar.

Ya kuma sa a tsare budurwar zuwa lokacin, a yayin da kotun za ta jira umarnin abin da zai biyo baya daga Ma’aikatar Shari’ar Jihar.