✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Bude makarantu: Iyaye sun yi bore kan kudin gwajin COVID-19

Sun ce ba za su biya N25,000 don a yi wa daliban gwajin COVID-19 ba, kawai don 'ya'yansu na karatu a makantun kudi

Iyayen daliban ajin karshe a makarantun sakandaren kudi a jihar Ogun sun yi zanga-zanga kan neman su biya N25,000 na gwajin cutar coronavirus a kan kowane dalibi.

Iyayen sun kai ‘ya’yansu Asibitin Kwararru MTR a garin Abeokuta domin gwajin ne kafin bude makarantu ga dalibai masu kammala sakandare a ranar Talata 4 ga watan Yuli.

Gwamnati ta shardanta wa kowane dalibi yin gwajin cutar da kuma gabatar da shaidar rashin kamuwa da ita kafin a shiga harabar makaranta.

Sai dai bayan zuwansu cibiyar gwajin sai aka ce musu kowane dalibin makarantar kudi zai biya N25,000, lamarin da ya fusata su.

Iyayen da daliban sun yi bore har suka rufe kokar shiga asibiin, tare da zargin mayar da gwajin cutar hanyar samun kudi.

Sun nemi dalilin bambanta ‘ya’yansu da takwarorinsu na makarantu gwamnati, alhali dukkaninsu yaran jihar ne mai ikirarin bayar da ilimi kyauta.

Dakta Kehinde Sanwo wanda shi ne Mataimakin Kungiyar Iyaye da Malamai ta PTA a makarantar Taidob College da ke Asero a Abeokuta, ya yi magana da ‘yan jarida a madadin iyayen.

“An ce za mu biya N25,000, alhali wadanda suka zo da farko ba su biya ko sisi ba. Daga ina umarnin ya zo? Wasunmu na da ‘ya’ya fiye da biyu. Mene ne dalilin bambancin?”

Sai dai Darekta a Ma’aikatar Lafiya ta jihar Dakta Olukayode Soyinka ya ce ba shi da masaniyar biyan N25,000 domin gwajin daliban makarantun kudi.

Ya ce gwajin COVID-19 kyauta, kuma kwamishinan lafiya na jihar, Dakta Tomi Coker ya umarce shi da ya tabbatar komai na tafiy daidai a cibiyar gwajin.

Ya ce ana yi wa daliban gwajin ne da daukar nauyin gwamnatin jihar tare da hadin gwiwar kamfanin 54gene.

Sai dai wani jami’in kamfanin na 54gene da wakilinmu ya tuntuba ya yi gum da bakinsa, bisa hujjar cewa ba shi da hurumin magana da ‘yan jarida.

Sai dai ya ce gwamnatin jihar ta ba wa kamfaninsa izinin gudanar da gwajin a cibiyar ta Asibitin Kwararru na MTR.