Assalamu Alaikum. Ya Mai Girma Shugaban Kasa, cike da girmamawa a gare ka, na rubuto maka wannan wasika ne domin inyi jinjina tare kuma da yin kira da kuma tsokaci akan wasu abubuwa da ke damun ‘yan Najeriya a sassa daban-daban na kasar nan. Daidai da ‘yancin fadin albarkacin baki wanda kundin tsarin mulkin kasar nan ya tanadar wa ‘yan kasa a sashe na 39.
Da farko, ina jinjina wa kwazon da kake yi wajen ganin daidaituwar al’amura a fadin kasar nan. Hakika, a cikin shekaru biyu da gwamnatin ka tayi, mu talakawan wannan kasa mun shaidi sauye-sauye masu ma’ana da kuma cigaba a fannoni daban-daban na rayuwa. Idan muka yi duba da yadda gwamnatin ka take mayar da hankali wajen tabbatar da walwala da jindadin ‘yan kasa ga baki daya. Kawo yanzu dai, mun shaidi nasarar da ka samu a fannin sha’anin tsaro, bunkasa harkar noma, samar da aikin yi, da kuma gina manyan tituna. Tabbas, ya zama wajibi a gare mu (Mu talakawa) mu yaba kuma mu yi Allah-sam-barka.
Sai dai kash ! Mai girma shugaban kasa, ra’ayin gwamnatocin jihohi ya shan bamban da ra’ayin gwamnati na inganta rayuwar talaka. Saboda, mafi yawan gwamnonin kasar nan suna yin gaban kan su ne kawai ba tare da la’akari da damuwar talakawan su ba.
Mai girma shugaban kasa, ma’aikata na fuskantar matsin lamba ko kuma in ce matsatsin tattalin arziki, wanda gwamnatocin juhohi ne suka haddasa musu da hakan. Biyan albashi ya zama karfen kafa a wasu jihohin. Wasu jihohin kuma korar ma’aikatan ma ake yi ba tare da la’akari da halin da ma’aikatan da aka kora daga aikin za su shiga ba.
A baya bayan nan ne, muka ji Gwamnatin Jihar Kaduna za ta sallami malamai sama da Dubu 21,000 daga aiki. Subhanallah! Mai girma shugaban kasa, babu wanda ya san iyakar mummunan halin da wadannan mutane za su tsinci kan su ba. Wasun su, magidanta ne masu aure. Wannan aikin ne suke rike rayuwar su da ta iyalinsu da shi. Alal hakika, Gwamna Nasiru Ahmad El-Rufa’i yana da zimmar kawo sauyi mai ma’ana da gyara na musamman ta fannin ilimi. Kuma lallai, bai kamata a bar malamai wadanda ba su cacanta ba, su cigaba da koyarwa a makarantu ba. To amma fa, matakin kora gaba daya daga aikin gwamnati, ya yi tsauri sosai. A kalla, ya kamata a dubi wani aikin koda na leburanci ne a ba su. Domin cigaba da rayuwa da kuma futar dasu kangin kaka-ni-ka-yi.
Mai girma shugaban kasa, lallai gwamnatin jiha ce ke da alhakin samar da hukumomin ta da kuma ma’aikatan ta, kuma ta kula da su, kamar yadda kundin tsarin mulkin kasar nan ya tanadar a sashe na 197 da kuma sashe na 2 karkashin tanadi na uku. To amma, ya kamata gwamnatin tarayya, ta yi duba a cikin wannan lamari domin samun daidaito. Hakika, duk wani dan kasa ya shaidi cewa, gwamnatinka, ta mayar da hankali sosai wajen yaki da rashin aikin yi a kasar nan. To kuma sai ga shi wannan mataki na gwamnatinka yana fuskantar tarnaki daga matakin gwamnatocin jihohi.
Ya Mai Girma shugaban kasa, a fannin jindadi da walwalar al’umma, shi ma yana fuskantar koma baya matuka. A inda wasu daga cikin gwamnonin tarayyar kasar nan suke rike albashin ma’aikatan su, ba tare da kwakkwaran dalili ba. Hakika, mun ji dadi sosai da aka ruwaito cewa, ka soma tattauna wannan matsala tare da su gwamnonin. To amma, har yanzu fa abin bai sauya. Saboda haka, nake amfani da wannan dama, domin in yi kira a gare ka, da ka rika bincikar yadda gwamnoni suke kashe kudaden da fadar ka take ba su domin yi wa talakawa ayyuka.
Bayan haka, Mai Girma Shugaban kasa, kamar yadda ka yi kira a koma gona domin samar da abinci da kuma habaka tattalin arzikin kasar nan. Tabbas, ‘yan kasa sun amsa wannan kira da ka yi mana, musamman ma matasa. Sai dai, kawo yanzu babu wani tallafin kayan noma da yake isko manoma kai tsaye daga fadar ka. Kamar takin zamani, iri da kuma sauran maganin kwari. Lallai, muna sane da cewa, abubuwa sun yi wa gwamnatin ka yawa, kuma mu talakawa mun sanya dogon buri a kan gwamnatinka, to amma, yana da kyau ka tuna cewa, mu talakawa mun sanya cikakkiyar yardar mu ne a kan ka kai kadai. Saboda haka nake kira, da a taimaka wa talakawa ta fannin noma.
Mai Girma Shugaban kasa, hakika, ka taka muhimmiyar rawa a fannin samar da ayyukan yi a tsakanin matasa. Musamman shirin N-Power wanda duk matashin da ya ci gajiyar shirin, zai samu kudi kimanin N720,000 a cikin watanni 24 domin ya zama mai dogaro da kansa. To amma, yana da kyau a duba fannin samar da cibiyoyin koyar da sana’o’in hannu a wasu jihohi, musamman yankin Arewa maso Gabas wanda suke cikin wani yanayin rayuwa ta daban, wasu daga cikin su ma, sun rasa sana’o’in su. Yin hakan zai taimaka matuka ainun wajen dawo da tattalin arzikin wannan yanki. Haka ma, wasu jihohi kamar Jihar Zamfara babu cibiyar koyon sana’o’i ko guda a fadin jihar.
Bayan haka, a fannin yakin da cin hanci da rashawa, wanda yake shi ne babban jigon gwamnatin ka. Mai Girma shugaban kasa, har yanzu fa, akwai salo daban-daban da cin hanci da rashawa da yake gudana a tsakanin al’umma. Misali, a bangaren daukar aiki a ma’aikatu (Musamman a ma’aikatun gwamnatin tarayya). Wanda yake, idan har babu sanayya ko kuma jagora, yana da wahala dan talaka ya samu aiki kai tsaye. Tabbas, ba lallai ne ace gwamnatin ka ta kakkabe sha’anin cin hanci da rashawa gaba daya ba. Amma dai, a kalla ya zama cewa, ka yaki cin hanci da rashawa, ya ragu da kamar kashi 70% cikin dari. A nan, zan so na yi kira a gare ka, da ka mayar da tsarin daukar aiki kamar yadda gwamnatin ka tayi a lokacin daukar ma’aikatan N-Power. Saboda, daukar wannan aiki ya kasance ne tiryan-tiryan kuma babu mugu-mugu a cikin sa. Hakan yasa ‘yan kasa suke yabawa da shi matuka ainun.
Mai Girma Shugaban kasa, da akwai sauran matsaloli da ke damun talakawan wannan kasa matuka. Amma a hankali zamu cigaba da fitowa ta kafafen yada labarai domin isar da sakon talakawa kai tsaye izuwa gare ka. Domin bayar da tamu gudunmawa ga cigaban kasa.
Da fatan za ka duba wadannan da dimbin damuwar al’ummarka don magance musu su.
A karshe, ina addu’ar Allah ya kara maka lafiya. Allah ya karfafe ka. Allah ya kara kawo mana zaman lafiya a Najeriya.
Amin Summa Amin.
Bissalam. Comrade Jibril Almustapha Gusau 08167628777 [email protected]