✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Budaddiyar wasika ga zababben Shugaban Kasa Tinubu

Budaddiyar wasika ga zababben Shugaba kasa Tinubu

Kafin in ce komai a kan wannan budaddiyar wasika gare ka, ya kamata in fara da rokon Allah Ya sa yadda aka yi zaben ranar 25 ga watan Fabrairun da ya gabata da ya kawo ka da sauran yan Majalisun Dokoki na kasa ga samun nasara lami lafiya gwargwadon zarafi, Allah Ya sa na gobe, inda za a zabi gwamnonin jihohi 28 da ‘yan Majalisun Dokokin jihohi 993, ya nunnunka naku samun irin waccan nasara, amin.

Ya zababben Shugaban kasa mai jiran gado, Alhaji Bola Ahmed Tinubu, ka dai san irin garwa da kwakwazo da hayaniyar da aka rika tafkawa a cikin jam’iyyar APC mai mulki da gwamnatin tsakiya, tun daga lokacin babban taron jam’iyyarka don fitar da gwanin da zai tsaya mata takarar neman shugabancin kasar nan a wancan babban zabe.

A wancan lokacin, in ka manta in tuna maka, in ban da gwamnonin jam’iyyarka na Arewacin kasar nan sun tsaya kai da fata a kan lallai kai za a zaba, da a yau labari ya sha bamban a kan a ce kai ne zababben Shugaban Kasar nan mai jiran gado.

Bayan nasararka a matsayin dan takarar jam’iyyarka, ka yi kundunbala ka dauki Sanata Kashim Shettima tsohon Gwamnan Jihar Borno daga shiyyar Arewa maso Gabas a matsayin mataimakinka, ta yadda ku biyun kuka kasance Musulmi.

Hadakar da ake ganin an wuce wurin a wannan zamani, bare ma har a ce an kai ga nasara. Shugabannin Kungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN) da wasu jiga-jigan jam’iyyarka mabiya addinin Kirista irin su tsohon Shugaban Majalisar Wakilai Mista Yakubu Dogara da tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya Mista Babachir Lawan, wadanda har kamfen din kar `yan kasa su amince da hadakarku, bare ma a zabe ku suka rika yi a sassa daban-daban na kasar nan. Baya ga kamfen din da limaman coci-cocin kasar nan suka rika yi majami’unsu.

Sakamakon nasararka ya tabbatar da cewa duk da kamfen din nasu bai yi tasiri a jihohinsu ba, amma dai ya yi tasiri a jihohi irin su Filato da Nasarawa da Babban Birnin Tarayya Abuja, dukkansu da suke cikin shiyyar Arewa ta tsakiya, shiyyar da ke dauke da mafi yawan Kiristoci da mabiya addinan gargajiya da arna marasa addini kowane iri na Arewacin kasar nan.

A jiharka ta Legas ma, wannan kamfen ya yi tasiri kasancewar jihar ta fada hannun dan takarar jam’iyyar LP dan kabilar Ibo kuma Kirista Mista Peter Obi, wanda ya ci wadancan jihohi biyu da Babban Birnin Tarayya Abuja na arewa da jihohin Edo da Delta da Kurosriba dake cikin shiyyar Kudu maso Kudu, inda kuma ake da `yan kabilarsa ta Ibo, baya ga jihohin shiyyarsa ta kudu maso gabas da ya yi maku shal. Duk da sunan banbancin kabila dana addini dana jinsi.

Samuwar hakan da ba a taba yi ba a tarihin siyasar kasar nan, yanzu ya shiga cikin kundin tarihin siyasar kasar nan har abada. Ya Shugaban kasa mai jiran gado, ban yi ma bayanin irin wahalhalu da kalubalen da ka yi ta fuskanta a cikin kamfen dinka ba, kamar maganar canjin fasalin wasu takardun kudin kasar nan da karancin man fetur, duk da suka faru a tsakiyar kamfen dinka, al`amarin da ya dugunzuma ka har ka kai ga fusata, ka yi zargin cewa ana ma kamfen dinka zagon kasa. Zargin da Gwamnatin Tarayya ta musanta.

Yadda ma Shugaba Buhari bai rinka binka kamfen dinka ba, kamar yadda kai ka yi masa a shekarun 2015 da 2019, da take-taken wasu daga cikin mukarrabansa da ake ma lakabi da Kabals, sun sa wasu magoya bayanka fassara haka tamfar shugaba Buhari ba ya goyon bayanka.

Na dan kawo ma ‘yan wadannan batutuwa ne, don su zama matashiya gareka da naka Kabals din idan ka hau kan karagar mulkin kasar nan. Duba da yadda sakamakon zaben ya kasance, ina fata kai da Kabals dinka za ku sa shi a cikin zukatanku, ta yadda ba za ku karkata wajen raya shiyyarka fiye da sauran shiyoyin kasar nan biyar, kamar yadda akai ta fargaban za ka yi kafin a zabeka.

Ya mai girma Asiwaju, na san dai ka fini sanin irin dimbin matsalolin da suke addabar kasar nan, ‘yan kasa kuma suke kyautata zaton ka magancesu, kama daga tabarbarewar matakan tsaro irin na ‘yan bindiga dana masu tada kayar baya da masu garkuwa da mutane don neman kudin fansa, baya ga rikicin ‘yan kungiyar Boko Haram dana ‘yan Neja Delta dana ‘yan haramtacciyar kungiyar masu neman tabbatar da kasar Biyafara ta IPOB da sauransu da aka dade ana fama da su.

Akwai kuma batun tabarbarewar ilimi da rashin aikin yi da talauci da suka yi ma `yan kasa kanta. Akan batun tabarbarewar ilimin nan, ina fata zaka yi ta maza wajen ganin ka fara da inganta ilimin bai daya, wato na Firamare wanda shike tushe, kafin ka yi batun na Sakandare zuwa na sauran manyan makarantu. Batun da ake yanzu akwai kananan yara kusan miliyan 20 da basu zuwa makarantun boko wadanda akasarinsu suna jihohin shiyyar Arewa maso Yamma (Kano da Zamfara da Jigawa Kaduna da Sakkwato da Katsina da Kabbi).

A kan batun rashin aikin yi da kididdigar Hukumar kididdiga ta kasa ta ce kashi 33.5, cikin 100, na yawan `yan kasa, a tsakankanin matasa kuwa ya kai kashi 42.5 cikin 100. Batun fatara da talauci kuwa yanzu an ce kusan kasar nan ita ce kan gaba da masu fama da matalauta a duniya baki daya, kasancewar kimanin mutum miliyan 133, daga cikin kusan mutum miliyan 220, suke fama da talauci kuma an ce karuwa suke.

Akwai kuma batun cin hanci da rashawa da ya yi wa kasar nan katutu, wanda kuma yake cikin muhimman batutuwan da Gwamnatin Shugaba Buhari ta sha alwashin kawo karshensa tun a kamfen dinta na shekarar 2015 amma kash! Sai ga shi har gwamnatin za ta sauka bayan mulkin shekara 8, hakar ba ta cin ma ruwa ba.

Inda ma ta tarar da ruwan ta bata shi, ya zama ruwan kashi. Ita da kanta ta yi kokari aka daure tsofaffin gwamnonin jihohin Filato da Taraba, Sanata Joshua Dariye da Rebaran Jolly Nyame amma kuma wane tudu wane gangare ita kuma da kanta, ta sake su da sunan afuwa. Sanin kowa ne, shiyyarka ta Kudu maso Yamma ita ta fi kowace shiyya amfana da ayyukan raya kasa na Gwamnatin Shugaba Buhari.

A mulkinka, ‘yan kasa musamman ‘yan Arewa sun zuba idanu su ga naka takun sakar, bisa ga irin yadda dama aka dade ana fargabar cewa ba za ka yi wa Arewa komai ba.

Daga karshe ina rokon Allah SWT Ya sanya mulkinka ya kawo zaman lafiya kwanciyar hankali da karuwar arziki da dukkan matsalolin kasar nan take fuskanta.